An Hango Tinubu Yana Kallon Yadda Aka Rantsar da Sabon Gwamnan Kogi Daga Faransa, Hotuna Sun Bayyana

An Hango Tinubu Yana Kallon Yadda Aka Rantsar da Sabon Gwamnan Kogi Daga Faransa, Hotuna Sun Bayyana

  • Shugaban kasa Tinubu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da hotunansa yana kallon bikin rantsar da Usman Ododo ya bayyana
  • Mai ba Tinubu shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya tabbatar da ci gaban sannan ya saki hotunan shugaban kasar a shafinsa na soshiyal midiya
  • Bayan rantsar da shi a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, Usman Ododo ya zama gwamnan jihar na biyar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

An gano Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kallon bikin rantsar da Gwamna Usman Ahmed Ododo na jihar Kogi, daga kasar Faransa.

Ku tuna cewa Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Faris, kasar Faransa, don kai ziyarar gashin kai a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Sabon mataimakin gwamnan Kogi ya durkusa a gaban Yahaya Bello bayan rantsar da shi, bidiyon ya yadu

Shugaban kasa Tinubu ya kalli bikin rantsar da Ahmed Ododo daga Faransa
An Hango Tinubu Yana Kallon Yadda Aka Rantsar da Sabon Gwamnan Kogi Daga Faransa, Hotuna Sun Bayyana Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Twitter

Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban kasar na musamman kan harkokin soshiyal midiya, ya tabbatar da hakan a shafinsa na X. Ana sa ran shugaban kasar zai dawo a makon farko na watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya halarci bikin rantsar da Ododo yayin da Tinubu ya kalli taron a talbijin daga kasar Faransa kuma hoto ya bayyana kan haka.

Mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

Ngelale ya rubuta:

"Mai girma Shugaban kasa Bola Tinubu ya kalli bikin rantsar da mai girma gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, a yau."

Mataimakin gwamnan Kogi ya duka gaban Bello

A wani labarin kuma, mun ji cewa Salifu Oyibo, sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi, ya dauki rantsuwar kama aiki a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki ya sake faruwa a Ibadan yayin da gobara ta tashi a ofishin INEC, an yi karin bayani

Jim kadan bayan rantsar da shi, an gano Oyibo a cikin wani bidiyo durkushe a gaban tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, yana mai nuna masa girmamawa.

An rantsar da mataimakin gwamnan ne kafin sabon gwamna, Usman Ododo, rahoton Punch.

Ododo ya bayyana kwamishinoninsa wajen rantsar da shi

A gefe daya, sabon gwamnan jihar Kogi da aka rantsar, Ahmed Usman Ododo, ya zabi yan majalisarsa da wasu manyan mukamai a wajen rantsar da shi.

Ododo, wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, ya gabatar da sunayen wasu kwamishinoninsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng