'Yan Bindiga da Yawa Sun Baƙunci Lahira Yayin da Suka Kai Hari a Jihar Arewa, Mutum 2 Sun Tsira
- Tsagerun masu garkuwa da mutane 3 sun bakunci ƙahira yayin musayar wuta da ƴan sanda a jihar Adamawa
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce dakarun sun ceto mutum 3 da maharan suka sace
- Ya ce lamarin ya faru ne bayan masu garkuwan sun kai hari wurin kiwon wani mutumi, inda suka tafi da mutum 2
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Wasu miyagun ƴan bindiga 3 masu garkuwa da mutane sun baƙunci lahira a jihar Adamawa da ke shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa dakarun ƴan sanda ne suka sheƙe su a wani samame da suka kai tare da taimakon mafarauta ƴan sa'kai.
Yayin wannan samame da jami'an tsaron suka fita, sun yi nasarar ceto mutum biyu da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su, Daily Post ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu.
Ya ce ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, 2024, ‘yan sanda suka ragargaji kungiyar miyagun a tsaunin Koma mai hade da garuruwan Kojoli da Karlahi na kananan hukumomin Jada da Fufore a Adamawa.
Yan sanda sun ceto mutum da aka sace
Kakakin ƴan sandan ya ci gaba da cewa:
"Jiya Laraba, masu garkuwa suka kai hari a wani wurin kiwon shanu na Alhaji Jibo Karlahi inda suka tafi da Umar Jibo mai shekaru 18 da Idi Hassan mai shekaru 13 a duniya.
"Nan take rundunar ƴan sanda ta tashi tawagar ceto suka bi sawun maharan. Daga ganin dakarunmu sai suka buɗe wuta aka fara musayar wuta. Sakamakon haka muka kashe 3 daga cikinsu.
"Amma sauran sun ari na kare ɗauke da raunukan harbin bindiga, abin farin cikin mun yi nasarar ceto mutum 2 da suka sato ba tare da an cutar da su ba."
A cewarsa, wannan nasara na ɗaya daga cikin ƙoƙarin rundunar na magance aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa, satar shanu, fashi da sauransu a jihar.
Sojoji sun gano abubuwan da suka haddasa rikicin Mangu
A wani rahoton kun ji cewa Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana muhimman abu 2 da suka jawo tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Mangu, jihar Filato.
Kakakin hedkwatar tsaro, Janar Buba, ya ce kisan da wani makiyayi ya yi wa ɗan garin Mangu na cikin abubuwan da suka jawo rikicin.
Asali: Legit.ng