An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma Da Wani Bisa Hannu a Yunkurin Kashe Kakakin Majalisa a Arewa

An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma Da Wani Bisa Hannu a Yunkurin Kashe Kakakin Majalisa a Arewa

  • Jami'an hukumar ƴan sandan Najeriya sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a yunƙurin kisan kakakin majalisar Benue
  • Mai magana da yawun yan sandan ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama har da shugaban ƙaramar hukuma
  • Ya ce ana zargin shugaban ƙaramar hukumar ne ya ɗauki hayar ƴan bindiga, ya ba su aikin kashe kakakin majalisa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar ƴan sanda cafke waɗanda ake zargi da hannu a kitsa makircin yunkurin kashe shugaban majalisar dokokin jihar Benuwai, Aondona Dajoh.

Daga cikin waɗanda ƴan sandan suka damƙe kan yunkurin kisan har wani shugaban ƙaramar hukuma guda a jihar da ke Arewa ta Tsakiya, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

Rundunar yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da yunkurin kashe kakakin majalisar Benue Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Rahoton binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa shugaban ƙaramar hukumar ne ya ɗauki hayar ‘yan bindiga da nufin su kashe Dajoh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

Yan sanda sun kama mutum biyu kan lamarin

A rahoton Vanguard, Adejobi ya ce:

"A kokarin dakarun rundunar ƴan sanda, sun yi nasarar cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan gillan, daga cikinsu har da wani shugaban ƙarar hukuma."
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa shugaban karamar hukumar ya ba wasu tsageru kwangilar kawar da kakakin majalisar dokokin jihar Benuwe, Aondona Dajoh."
"Dakarun sashin tattara bayanan sirri na rundunar ƴan sanda nan take suka kai ɗauki bayan samun bayanan sirri kan yunkurinsu na aikata kisan kai.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta lakume kayayyakin miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar jihar Arewa

A karshe kakakin ƴan sandan ya ƙara da bayanin duk waɗanda aka kama kan zargi a wannan lamarin zai fuskanci fushin doka ko shi wanene.

Rundunar ƴan sandan ta kuma tabbatarwa ɗaukacin al'ummar Najeriya cewa dakaru ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen a kokarin tabbatar da bin doka da oda.

Yan bindiga sun sace mutane 31 a Katsina

A wani rahoton kuma Yan bindiga sanye da kakin soji sun yi awon gaba da bayin Allah sama da 30 a yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun yaudari jama'a da sunan jami'an tsaro ne aka turo su ba su kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262