Abuja: Dakarun Yan Sanda Sun Ragargaji Ƴan Bindiga, Sun Ceto Wani Bawan Allah Tare da Kama 1

Abuja: Dakarun Yan Sanda Sun Ragargaji Ƴan Bindiga, Sun Ceto Wani Bawan Allah Tare da Kama 1

  • Dakarun ƴan sanda sun ceto Suleiman Sabo, wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a birnin Abuja
  • Kwamishinan ƴan sandan FCT, Haruna Garba, ya ce yayin ceto mutumin, yan sanda sun kama mutum ɗaya da ake zargi ɗauke da bindiga
  • Baya ga Sabo, mazauna Abuja da dama da ke hannun masu garkuwa da mutane sun kuɓuta a karshen makon nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An ceto Suleiman Sabo, mazaunin babban birnin tarayya (FCT) da aka yi garkuwa da shi a yankin Sauka da ke titin filin jirgin sama na Abuja ranar Juma'a.

Rahoton ya nuna cewa Sabo na kan hanyar komawa gida shi da matarsa, kwatsam ƴan bindigan suka tare motar da suke ciki, suka yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Yan sanda sun ceto wanda aka sace a Abuja.
Yan Sanda Sun Ceto Mutumin da Yan Bindiga Suka Sace a Birnin Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

An tattaro cewa mutumin na tuƙa motarsa mai suna Lexus Jeep mai lamba ABC 769 TP a lokacin da lamarin ya rutsa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a ranar Lahadi, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna Garba, ya bayyana cewa an yi nasarar ceto Sabo daga hannun masu garkuwa.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja, ya ce dakarun ‘yan sanda na ofishin Iddo a kauyen Sauka ne suka ceto mutumin.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da rundunar ƴan sandan Abuja ta wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter.

'Yan sanda sun kama mutun ɗaya da ake zargi

Ya ce an kama wani Muhammed Abel dan asalin jihar Kogi a yayin ƙoƙarin ceto Mista Sabo, inda ya ce an kwato bindiga guda da harsashi guda goma a hannunsa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sako ƙarin mazauna Abuja da suka yi garkuwa da su, sun turo saƙo

A cewar kwamishinan ƴan sandan, wanda aka ceto ya samu wasu raunuka a hannun masu garkuwar da mutanen kuma a halin yanzu yana samun kulawar likita.

CP Garba ya ƙara da bayanin cewa da zaran ya samu cikakkiyar lafiya za a damƙa shi hannun iyalansa.

Da yake nanata kudurin rundunar na tsaftace FCT daga aikata laifuka, ya bukaci mazauna yankin da su kai rahoton abubuwan da suke zargi ga jami'an tsaro.

Baya ga Sabo, wasu mazauna Abuja da aka sace a farkon watan Janairu, sun sami 'yanci a karshen makon nan.

Wani abun fashewa ya tashi a Kaduna

A wani labarin Rahotanni sun bayyana cewa wani abu da ake zargin 'Bam' ne ya tashi a garin Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa a bayanan da ta samu daga jami'an tsaro, mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu 10 suka ji rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262