Abdulsamad Rabiu Ya Samu Sabon Matsayi a Jerin Attajiran Duniya Bayan Ya Zarce Mike Adenuga
- Abdulsamad Rabiu ya zarce Mike Adenuga inda ya sake zama a matsayin mutum na biyu mafi arziƙi a Najeriya
- Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shugaban kamfanin na Globacom ya samu wannan kambun sakamakon ƙaruwar dukiyarsa
- Yanzu an kiyasta dukiyar Rabi'u ta kai dala biliyan 7.2 inda ya zama na 343 a jerin masu kuɗin duniya na Forbes
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Abdulsamad Rabi'u ya ga darajar dukiyarsa ta samu ƙaruwa sosai, inda ta kai shi wani sabon matsayi a cikin jerin hamshaƙan attajiran Najeriya.
Rabiu ya zama attajiri na biyu a Najeriya bayan Aliko Dangote, kuma ya kai matsayin mutum na biyar mafi arziki a Afirika.
Attajirin ya dawo da matsayinsa na mutum na biyu mafi arziki a ƙasar nan bayan da arziƙinsa ya ƙaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu ya zarce Adenuga
Mujallar Forbes ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairun 2024, arzikin Rabiu ya ƙaru da dala biliyan 1.5, inda ya kai dala biliyan 7.2.
Da wannan ƙaruwar arziƙim, Rabiu ya zarce hamshaƙin attajirin nan Mike Adenuga mai kamfanin sadarwa na Globacom, wanda a kwanakin baya ya samu dala biliyan 7.4.
Tun daga ranar 11 ga watan Janairu, arzikin Adenuga ya ragu matuƙa, inda ya yi ƙasa da dala miliyan 400 zuwa dala biliyan 7.
Mike Adenuga ya zama attajiri na biyu a Najeriya a gaban Abdulsamad Rabiu wanda ya koma na uku.
Billionaire Africa ta ruwaito cewa, kasuwancin Rabi'u a kamfanonin simintin BUA da na abincin BUA, sun taka rawar gani, wanda ya ba da gudummawar ƙaruwar dala biliyan 1.5 a dukiyarsa.
Rabiu dai shine na biyu mafi arziki a Najeriya
Rabiu dai ya zama attajiri na biyu a Najeriya bayan Aliko Dangote kuma ya kai matsayi na biyar a duniya.
Rabiu ya zo na 344 a jerin attajiran duniya da Forbes ta fitar inda yanzu haka aka kiyasta cewa ya kai dalar Amurka biliyan 7.2 har zuwa lokacin wannan rahoton.
Arziƙin Dangote Ya Ƙaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirika, Aliko Dangote ya ƙara yin sama da matsayi 56 a jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya.
Dangote yanzu ya zama mutum na 137 a cikin jerin attajiran duniya daga matsayi na 192 da yake a kai a ranar Talata, 10 ga Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng