Ibadan: Adadin Mutanen da Suka Mutu Yayin da Wani Abu ya fashe a babban birnin jihar PDP ya ƙaru
- Gwamnatin Oyo karkashin Gwamna Makinde ta yi ƙarin haske kan yawan mutanen da suka mutu a fashewar da ta afku a Ibadan
- Mai ba gwamna shawara na musamman kan tsaro, Fatai Owoseni, ya ce adadin mamatan ya ƙaru zuwa 5 a yau Alhamis da safe
- Ya jaddada cewa jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu don tabbatar da duk mai hannu ya girbi abinda ya shuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya afku a Bodija, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya ƙaru zuwa biyar.
Gwamnatin Oyo karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ce ta bayyana haka ranar Alhamis, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Fatai Owoseni, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro ne ya yi wannan ƙarin hasken yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin gwamnan ya tabbatar da cewa an gano ƙarin gawarwakin mutum biyu, wanda jimulla an samu gawar mutum 5 kenan sakamakon ibtila'in.
Mista Oweseni ya ce:
"Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, a jiya mun gano gawarwakin mutum uku amma zuwa yau da safe, mintunan 30 da suka wuce na samu ƙarin bayani daga jami'an tsaro.
"Jami'an tsaron waɗanda ke taimaka wa tawagar likitoci a wurin sun shaida mun cewa an ciro ƙarin gawar mutane biyu da safiyar nan. Ana ta maganganu yayin da gwamnati ke ci gaba da aiki a buɗe kowa ya gani."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Dangane da matakin da gwamnati ta ɗauka kuwa, ya ce jami'an tsaro da suka kunshi ƴan sanda, DSS sun haɗa kai da sojoji domin tabbatar da duk mai hannu a fashewar ya shiga hannu.
A cewarsa, jami'an tsaron haɗin guiwar na aiki tukuru domin ganin duk wanda ke da hannu a kitsa wannan lamarin, ya fuskancin fushin doka, Channels tv ta rahoto.
An sace basarake da matasa a Kwara
A wani rahoton kuma Wasu mahara da ake zaton ƴan bindiga ne sun sace wani basaraken ƙauye da matasa uku a jihar Kwara.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro sun cafke mutum 3 da ake zargi da hannu a harin.
Asali: Legit.ng