Kotu Ta Amince da Sabuwar Bukatar Emefiele, Ta Sanya Sharadi 1
- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya samu nasara a babbar kotun tarayya da ke Abuja
- Kotun a safiyar yau Alhamis ta amince da buƙatar Emefiele ta a bar shi ya yi tafiya zuwa wajen birnin tarayya Abuja
- A yayin amincewar buƙatar tsohon gwamnan na CBN, kotun ta gindaya masa sharaɗin cewa kada ya yi tafiya zuwa wajen ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta amince da buƙatar tohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.
Kotun ta amince da buƙatar da Emefiele ya gabatar a gabanta ta neman a bar shi ya yi tafiya zuwa wajen babban birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.
Tsohon gwamnan na CBN dai yana fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume shida da suka shafi zambar kwangilar siyo kayayyaki waɗanda kuɗinsu ya kai N1.2bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta amince da buƙatar Emefiele
Jaridar The Punch ta bayyana cewa a safiyar ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu tsohon gwamnan na CBN ta hannun lauyansa Mathew Bukka ya buƙaci kotun da ta sassauta sharuɗɗan belinsa.
A belin da kotun ta ba Emefiele dai, ta hana shi barin babban birnin tarayya Abuja.
Mai shari'a Hamza Mu'azu a yayin amincewar da buƙatar ta Emefiele, ya gindaya masa sharaɗin cewa kada ya kuskura ya bar ƙasar nan.
An saki Emefiele daga gidan gyaran hali na Kuje a ranar 23 ga watan Disamban 2023, kwanaki 34 bayan alƙali ya amince da bayar da belinsa kan kuɗi har N300m.
Buhari Ya Fadi Dalilinsa Na Ƙin Korar Emefiele
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sanya bai kori Godwin Emefiele ba daga muƙaminsa na shugaban babban bankin Najeriya (CBN), a lokacin mulkinsa.
Buhari ya bayyana cewa korar Emefiele a lokacin zai zama zalunci ne da rashin adalci saboda bai taɓa gaya masa aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa ba a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng