Duk da Wuyar da Aka Sha, Buhari Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Ki Korar Emefiele Daga Shugabancin CBN

Duk da Wuyar da Aka Sha, Buhari Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Ki Korar Emefiele Daga Shugabancin CBN

  • Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce bai kori Godwin Emefiele daga muƙamin gwamnan CBN ba saboda bai taɓa tattaunawa da shi kan kuɗurinsa na takarar shugaban ƙasa ba
  • Buhari ya ce rashin adalci ne da zalunci a kori Emefiele a kan abin da mutane ke jita-jita a kansa
  • Ya kuma ce tsarin da gwamnatinsa ta yi na sake fasalin Naira ya taimaka wa ƙasar nan wajen ganin an gudanar da zaɓe mai tsafta a 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai kori tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ba a lokacin da ake ta cece-kuce akan ƙudirinsa na yin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar CCB? Gaskiya ta bayyana

Buhari ya ce Emefiele bai taɓa tattaunawa da shi kan wani ƙudiri na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ba, cewar rahoton The Nation.

Buhari ya fadi dalilin kin korar Emefiele
Buhari ya yi magana kan dalilin kin korar Godwin Emefiele Hoto: Muhammadu Buhari/CBN
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wani littafi mai suna “Working with Buhari: Reflections of a Special Adviser Media and Publicity (2015 – 2023)” wanda aka ƙaddamar a ranar Talata, 16 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Buhari ya ƙi korar Emefiele

A kalamansa:

"A lokacin da na hau mulki na tarar da Emefiele a ofis, sannan idan ba an samu ƙwararan hujjoji a kansa ba, zai zama zalunci da rashin adalci kore shi, ta hanyar amfani da jita-jita."

Ya ƙara da cewa:

"Lokacin da aka alaƙanta shi da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a 2023, ban tambaye shi ba, saboda bai gaya wa kowa cewa yana takara ba. Idan ba haka ba, da na cire shi na gaya wa al’umma dalilin da ya sa."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Manufar sake fasalin Naira ya taimaka a zaɓen 2023

Akan manufofin sake fasalin Naira, Buhari ya ce:

"Babu musun cewa manufar sake fasalin Naira ta ba mu zaɓe mai tsafta. Mutanen da ke da kuɗi da yawa ne suka sami matsala da shi.
"Lokacin da aka ce ba a samu sabbin takardun kuɗin ba, an samu sama da Naira miliyan 260 a wajen wani shugaban banki."

Buhari Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan wasu matakai da ya ɗauka a gwamnatinsa.

Tsohon shugaban ƙasar ya amince cewa ya kawo tsare-tsaren da suka wahalar da al'umma, amma ba don su tagayyara ya yi hakan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng