Gwamna Makinde Ya Bayyana Abin da Ya Haddasa Tashin Abin Fashewa a Ibadan, Bidiyo Ya Bayyana
- Gwamna Seyi Makinde ya tabbatar da cewa binciken farko ya nuna cewa wasu masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ne suka haddasa fashewar wani abu a Ibadan
- Makinde, a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Laraba, ya ce mutum biyu sun mutu sannan wasu mutum 77 sun samu raunuka
- Gwamnan ya bayyana ewa gwamnatin jihar za ta biya kuɗaɗen jinyar waɗanda suka jikkata, tare da samar da masauki na wucin gadi ga waɗanda abin ya shafi gidajensu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa abin fashewar da ya girgiza babban birnin jihar Ibadan, a daren ranar Talata, na iya zama aikin masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a jihar.
A cikin wani bidiyo, Makinde ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wasu masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, sun aje abubuwan fashewa a ɗaya daga cikin gidajen da fashewar ta auku.
A cikin wani rubutu a shafinsa na Twitter da safiyar ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, gwamnan ya ce ya ziyarci wajen da asibitocin da aka kwantar da waɗanda suka jikkata sakamakon aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin sani dangane da abin da ya fashe a Ibadan
Gwamna Makinde ya kuma tabbatar da cewa mutum biyu ne suka mutu sakamakon lamarin sannan mutum 77 sun samu raunuka. Suna karɓar magani a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu dake faɗin babban birnin jihar.
Makinde ya ƙara da cewa, ya umurci cewa gwamnatin jihar ta biya kuɗaden jinyar waɗanda suka samu raunuka, kuma waɗanda abin ya shafa za a samar musu da wurin kwana na wucin gadi yayin da gwamnati za ta tallafa wajen sake gina gidajensu.
A kalamansa:
"Bincike na farko da jami'an tsaro suka gudanar ya nuna cewa masu haƙar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ke zama a ɗaya daga cikin gidaje a Bodija sun ajiye abubuwan fashewa a wurin, wanda hakan ya haifar da fashewar.
"Ana cigaba da gudanar da bincike, duk waɗanda aka samu da hannu a wannan lamarin za su fuskanci fushin hukuma."
Abin Fashewa Ya Kashe Mutane a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wani abin fashewa a garin Galkogo dake ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu bayan abin fashewar ya tarwatse a cikin garin.
Asali: Legit.ng