Mutane Sun Shiga Fargaba Sakamakon Tashin Abin Fashewa a Ibadan, Bidiyo Ya Fito
- Kayayyaki da dama sun lalace a unguwar Bodija na Ibadan, jihar Oyo, bayan tashin wani abin fashewa a harabar Domino Pizza
- Legit Hausa ta rahoto cewa duk da a hukumance ba a tabbatar da rasa rai ba, fashewar ya razana mutane a garin
- Yayin da wasu ke cewa tukunyar gas ne ya fashe, wasu kuma sun ce harin bam ne aka kai wa masu shagunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Ibadan, jihar Oyo - An ji wani kara mai karfi sakamakon tashin abin fashewa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Legit Hausa ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 16 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Punch ta rahoto, an ji karar mai karfi kusa da yankunan Agbowo, Orogun da Bodija a garin.
Sai dai, a riga an gano musabbabin tashin abin fashewar ba a lokacin hada wannan rahoton.
Wani mazaunin Orogun, kusa da Jami'ar Ibadan (UI) ta fadawa Legit.ng cewa:
"Na gano cewa ya faru a harabar Domino Pizza a unguwar Bodijia. Ya girgiza unguwanni da dama a Ibadan. Na kuma ji cewa ya lalata gine-gine masu yawa.
"Mutane a Apete, Omi Adio, Mokola, sun ji girgizan fashewar."
Wani majiya daban a Agbowo ya ce ya samu labarin cewa tukunyar gas ce ta fashe.
Wani mai amfani a manhajar X (tsohuwar manhajar Twitter), @WillieWinehouse, ya ce bam ne ta tashi.
Sai dai, Legit Hausa ba ta iya tabbatar da ikirarin da mutanen biyu suka yi ba.
Kokarin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Adewale Osifeso, bai yi nasara ba.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng