Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Kwamishina Ya Rasu Kwanaki Kaɗan Bayan Rasa Muƙaminsa a Arewa
- Gwamna Yahaya Bello ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kogi, Kwamared Yahaya Adesayo
- Tsohon kwamoshinan wanda bai jima da sauka ba ya mutu ne da yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Janairu kuma an masa jana'iza a musulunce
- Bello ya bayyana cewa marigayin aboki ne na gari, wanda ya tsaya tare da shi a tsawon lokacin da ya shafe yana siyasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman da ya gabata a jihar Kogi, Kwamared Yahaya Adesayo Isma'il, ya riga mu gidan gaskiya.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Allah ya yi wa Isma'il rasuwa ne da yammacin jiya Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024.
Yana ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwar Yahaya Bello har zuwa makon da ya gabata sa'ilin da gwamna mai barin gado ya sallame su daga aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa tsohon kwamishinan na cikin koshin lafiya babu ciwon da ke damunsa har zuwa yammaci jiya Litinin da aka samu labarin cewa Allah ya masa rasuwa.
Gwamna Bello ya miƙa sakon ta'aziyya
A halin yanzu dai Gwamna Bello ya bayyana rasuwar tsohon kwamishinansa a matsayin "rasuwar da ta zo a lokacin da ba a yi zato ba."
A kalamansa, Gwamna Yahaya Bello ya ce:
"Ya kasance amintaccen mutum wanda ya gudanar da rayuwarsa kan bin tafarkin Allah SWT da kuma taimakon al'umma tare da nuna kauna da tausayi ga kowa."
Tsohon kwamishina ya mutu a Benue
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tsohon kwamishina a tsohuwar jihar Benuwai, Alhaji Shehu Usman, ya rasu yana da shekara 91 a duniya.
Othman ya rasu ne a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, a asibitin Trust Charitos dake Jabi, Abuja, bayan gajeruwar rashin lafiya, rahoton Daily Trust.
Iyalansa sun tabbatar da rasuwar a wata sanarwa inda suka yi nuni da cewa za a yi jana’izar marigayin a ranar bayan Sallar Azahar a babban masallacin kasa dake Abuja.
Wata mata da jama'a ke kauna ta mutu
A wani rahoton kuma Allah ya yi wa fitacciyar ma'aikaciyar radiyo da mutane ke ƙauna a Abuja rasuwa.
Matashiyar ra rasa rayuwarta ne yayin wata babbar mota maƙare da ya shi ta yi karo da motarta a titin filin jirgin saman Abuja.
Asali: Legit.ng