Dangote Ya Samu Sabon Matsayi a Jerin Attajiran Duniya Bayan Arzikinsa Ya Karu da N227bn a Sa'oi 24

Dangote Ya Samu Sabon Matsayi a Jerin Attajiran Duniya Bayan Arzikinsa Ya Karu da N227bn a Sa'oi 24

  • Aliko Dangote ya ƙara sama da matsayi 56 a jerin attajiran duniya kuma yanzu ya kusa shiga cikin 100 na farko
  • Sabbin bayanai sun nuna cewa arziƙin attajirin da yafi kowa arziƙi a Najeriya ya ƙaru da sama da Naira biliyan 217 cikin sa'o'i 24
  • Wannan ƙaruwar arziƙin da Dangote ya samu ta faru ne sakamakon yadda kamfanin simintinsa ke samun tagomashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirika, Aliko Dangote ya ƙara yin sama da matsayi 56 a jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya.

Dangote yanzu ya zama mutum na 137 a cikin jerin attajiran duniya daga matsayi na 192 da yake a kai a ranar Talata, 10 ga Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fara shirin yin wani abu 1 domin faranta ran yan Najeriya lokacin azumi

Arzikin Aliko Dangote ya karu
Dangote ya kara sama a jerin attajiran duniya Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Arziƙin attajiran Afirika ya sake farfaɗowa a cikin ƴan kwanakin da suka gabata bayan fara sabuwar shekara a matsayi mafi ƙaranci a wajensu cikin shekaru 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arziƙin Dangote ya ƙaru da dala miliyan 229

A cewar rahoton Forbes, dukiyar Dangote ta ƙaru da dala miliyan 229 (sama da Naira miliyan 217) a ranar Laraba 11 ga watan Janairu inda ta kai dala biliyan 13.8 idan aka kwatanta da dala biliyan 10.3 da take a ranar Talata.

Wannan ƙaruwa ta nuna yadda kamfanoninsa ke samun tagomashi a kasuwar zuba jari ta Najeriya.

Wani bincike da Legit.ng ta yi ya nuna cewa hannun jarin siminti na Dangote ya ci gaba da ƙaruwa tsawon kwanaki uku.

Hannun jarin kamfanin wanda ya fara sabon makon nan a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu a kan N325, ya ƙaru zuwa N350 kan kowanne hannun jari.

Kara karanta wannan

Betta Edu: An bayyana abu 1 da ya kamata yan Najeriya su yi wa dakatacciyar ministar Tinubu

Hakazalika, wani daga cikin kamfanoninsa, Sikarin Dangote, ya ga farashin hannun jarinsa ya tashi daga Naira 65 a ranar Litinin zuwa Naira 67.5 kan kowanne hannun jari a ranar Laraba.

Arziƙin Dangote zai ƙara bunƙasa yayin da matatar man fetur ɗinsa mai samar da ganga 650,000 ke shirin fara aiki.

Dangote Ya Yi Ƙasa a Jerin Attajiran Afirika

A baya rahoto ya zo cewa Aliko Dangote ya sulluɓo daga matsayin attajiran da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirika.

Dangote ya koma matsayin na biyu bayan attajirin ƙasar South Africa ya doke shi daga matsayin wanda yafi kowa kuɗi a Afirika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng