Babban banki CBN Ya Kori Dukkan Daraktocin Bankuna 4 a Najeriya, Bayanai Sun Fito
- CBN ya rushe majalisar daraktocin bankuna huɗu a Najeriya bayan sunayensu sun shiga rahoton binciken Emefiele
- A wata sanarwa da babban bankin ya fitar ranar Laraba, ya ce ya ɗauki matakin ne saboda bankunan sun saɓa kundin doka
- Rahoton binciken da Tinubu ya sa aka yi ya nuna cewa tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya mallaki wasu bankuna ta hanyar wakilai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya kori daukacin majalisar gudanarwar bankunan Polaris, Titan Trust, Union da Keystone nan take.
Daraktan sadarwa na CBN, Sidi Hakama, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba kuma bankin ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.
CBN ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne sabida rashin bin dokar da waɗannan bankuna da kuma majalisar daraktocinsu suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwan, "ɗaukar wannan matakin ya zama dole saboda kunnen ƙashin wadannan bankuna da daraktocin su tare da take tanadin sashe na 12 (c), (f), (g), (h) na kundin dokokin bankuna 2020.”
CBN ya kuma bai wa jama’a tabbacin tsaron kudaden da suka ajiye a bankunan, inda ya jaddada kudirinsa na inganta tsarin hada-hadar kudi a Najeriya.
Asalilin dalilin ɗaukar wannan mataki
Binciken da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sa aka yi a CBN lokacin tsohon gwamna, Godwin Emefiele, ne ya gano cewa akwai ayar tambaya a kan waɗannan bankuna.
Bayan dakatar da Emefiele a watan Yuni, Tinubu ya nada Jim Obazee a matsayin mai bincike na musamman a CBN.
A rahoton da ya mika wa shugaban kasa, Obazee ya ce Emefiele ya yi amfani da “dukiyar haram” wajen kafa TTB sannan ya mallaki bankin Union da Keystone ta hannun ‘yan amshin shatansa.
Rahoton ya kuma tuhumi wani marigayi makusancin tsohon shugaban kasa Buhari, Ismaila Isa Funtua, da laifin saye bankunan Keystone da Polaris.
Mista Obazee ya ba da shawara a rahoton bincikensa cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta karɓe waɗannan bankuna.
Da gaske EFCC ta damƙe shugaban Ja'iz?
Kuna da labarin cewa a yayin da ake ci gaba da bincike kan badakalar dakatacciyar Ministar jin kai, Betta Edu, abin ya fara girma.
Ana tuhumar wasu bankuna da zargin karbar makudan kudade daga ma'aikatar jin kai ciki har da Ja'iz.
Asali: Legit.ng