Tsohuwar Ministan Buhari, Sadiya Farouq, Ta Kai Kanta Ofishin EFCC
- Sadiya Umar-Farouq, ministar jin kai a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta mika kanta ga hukumar EFCC
- Tun a makon da ya gabata ne aka yi tsammanin Umar-Farouq za ta mika kanta, amma ta sanar da hukumar ba ta da isasshiyar lafiya
- Hukumar EFCC ta nemi ganawa da tsohuwar ministar don yi mata wasu tambayoyi kan wata badakalar naira biliyan 37.1 da ta ke bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A karshe dai tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar-Farouq, ta mika kanta domin bincike a hedikwatar hukumar EFCC da ke Abuja.
Tsohuwar ministar, wadda ake tuhumar ta da karkatar da kudi har naira biliyan 37.1 ta hannun wani dan kwangila, James Okwete, ta isa ofishin EFCC ne a safiyar ranar Litinin.
Umar-Farouq ta wallafa a shafinta na Twitter:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A bisa ga ra'ayi na, na isa hedikwatar hukumar EFCC domin karrama goron gayyata da hukumar ta yi mun na bayar da karin haske kan wasu batutuwan da hukumar ke bincike a kansu."
EFCC za ta tuhimi Umar-Farouq kan zargin karkatar da kudi
A baya dai Umar-Farouq ta ki amsa gayyatar da EFCC ta yi mata, inda ta roki a kara mata lokaci saboda rashin lafiyar da ta ke fama da ita, Trust TV News ta ruwaito.
A makon da ya gabata, Dele Oyewale, kakakin hukumar EFCC ya ce tsohuwar ministar jin kai, ta aike wa hukumar wasika na dalilin rashin amsa gayyatar da suka yi mata.
A yanzu da ta mika kanta, hukumar EFCC za ta tuhume ta kan badakalar naira biliyan 37,170,855,753.44, da ake zargin an karkatar da su ta karkashin ofishin ta a zamanin Buhari.
"Ki kawo kanki tun muna shaidar juna", EFCC ta gargadi Sadiya
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa hukumar EFCC ta ce ba za ta ci gaba da lamuntar kin bayyanar Sadiya Umar-Farouq a ofishinta ba.
Mr Dele Oyewale, kakakin hukumar ya ce EFCC ba za ta daga wa Umar-Farouq kafa ba, don haka ta ajiye batun rashin lafiya ta mika kanta tun suna ganin girman juna.
Asali: Legit.ng