'Yan Bindiga Sun Bukaci Naira Miliyan 60 Fansar Yara 6 Da Suka Sace a Abuja
- Yan bindiga da suka sace wani Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da yaransa shida sun kira dangin su
- Masu garkuwa da mutanen sun bukaci sai dai a biya naira miliyan 60 na fansa kafin su sako yaran su shida
- Tuni suka sako mahaifin nasu domin ya zo ya nemi kudin fansar yaransa da ke hannunsu har yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Yan bindigar da suka yi garkuwa da Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da yaransa shida sun tuntubi yan uwansu, inda suka bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 60.
An yi garkuwa da mutanen ne a daren ranar Talata a yankin Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, rahoton Daily Trust.
Yan bindigar sun harbe dan uwan mutumin mai suna Alhaji Abdulfatai, wanda shine ya jagoranci jami'an yan sanda don dakile sace su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, an rahoto cewa biyu daga cikin jami'an yan sanda uku da harbi ya sama yayin musayar wuta sun kwanta dama.
Yan bindigar sun sako mahaifin yaran don ya nemi kudin fansa
An kuma tattaro cewa yan bindigar sun sako mahaifin daga baya domin ya koma ya nemo kudin fansa don sakin yaransu, rahoton Solacebase.
Bayan faruwar wannan sabon lamari, iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, daga yankin Okekere da ke Ilọrin, babban birnin jihar Kwara, sun fara neman kudi a ranar Lahadi domin ceto su.
Da ake zantawa da shi a wata hira ta wayar tarho, wani dan uwan wadanda abin ya shafa, Sherifdeen, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai cike da kalubale ga iyalin.
Ya ce:
“Sun tuntubi iyalin suna neman kudin fansa naira miliyan 60 bayan sun dade suna rokonsu. Sun saki mahaifin amma sun tsare yaran. An ba mu Juma'a, 12 ga watan Janairu, 2024 don nemo kudin.
"Naira miliyan 10 kenan kan kowani yaro. Domin taimakawa a kokarin da ake yi na ceto su, muna neman taimakon kudi. Mun bayar da bayanan banki a shafina na Facebook.
"Yayin da muke jiran ji daga wajen masu garkuwa da mutanen, muna neman addu'arku kan sako masoyanmu cikin koshin lafiya sannan muna godiya da duk wani taimakon kudi a wannan lokaci mai cike da kalubale."
Yan bindiga sun sace basarake
A gefe guda, mun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Imo, Mai martaba Eze Samuel Agunwa Ohiri.
An rahoto cewa an yi garkuwa da basaraken ne a gaban gidansa da ke Orodo, karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, da misalin karfe 8:30 na safiyar Asabar, 6 ga watan Janairu, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng