Yara, da Mata Sun Mutu Yayin Jirgin Ruwa Ya Kife a Rafin Niger
- An rahoto cewa an fargabar wasu mutane da suka hada da mata da yara sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Rafin Niger da ke Anambra
- Wadanda abin ya faru da su, wanda yanzu ba tantance adadinsu ba, sun fito ne daga Jihar Kogi lokacin da abin ya faru a safiyar ranar Lahadi a gabar Onitsha
- Tochukwu Ikenga, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Anambra, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa tuni an fara bincike
Mutane da dama ciki har da mata da yara, a cikin wani jirgin ruwa da ba a tabbatar da sunansa ba ana fargabar sun mutu lokacin da jirginsu ya kife a Rafin Niger.
A cewar The Punch, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi, 7 ga watan Disamba, a yayin da aka gano wasu yan Najeriya na ceto wadanda abin ya faru da su a gabatar Onitsha.
An gano hakan na cikin wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin rubuta wannan rahoton, ba a riga an tabbatar da adadin wadanda suka rasu ba, amma an gano fasinjojin sun fito ne daga jihar Kogi.
Yan sanda sun tabbatar da hatsarin jirgin ruwan
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya kara da cewa a halin yanzu an shawo kan lamarin.
Kakakin yan sandan ya ce jami'an sojojin ruwa sun amsa kirar neman dauki cikin gaggawa daga suka samu daga yankin.
Wani sashi na sanarwarsa ta ce:
"Binciken farko ya nuna cewa jirgin ya fito ne daga Jihar Kogi, yana dauke da kayayyaki da fasinjoji kafin abin bakin cikin ya faru."
Ikenga ya ce kawo yanzu ba a gano sanadin afkuwar hatsarin, ya kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike.
Mutum Biyu Sun Rasu, Huɗu Sun Samu Rauni Yayin da Jirgin Ruwa Ya Kife a Legas
A wani rahoton, mutane biyu sun rasu, wasu huɗu sunyi rauni yayin da wani jirgin ruwa ya kife da mutane a kauyen Isawo da ke karamar hukumar Ikorodu ta jihar Legas.
Ololade Agboola, mataimakin kakakin hukumar kashe gobara da ayyukan ceto na jihar Legas, ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng