Yan Sanda Sun Kama Malamin Addini Bisa Zargin Haikewa Matashiya a Ogun

Yan Sanda Sun Kama Malamin Addini Bisa Zargin Haikewa Matashiya a Ogun

  • Iyayen matashiyar budurwar sun lura an taba ta ne bayan da suka fara ganin sauyi a tattare da ita
  • Faston, wanda ya sanar da jami'an tsaro gaskiyar lamari, ya ce bai san adadin kwanciyar da ya yi da yarinyar ba
  • Tuni rundunar yan sanda ta cafke malamin addinin tare da ci gaba da binciken sa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da kama wani malamin addini, Fasto Clinton John, bisa zarginsa da cin zarafin wata yarinya, da aka bukaci a sakaya sunanta, a yankin Agbado dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Ota, a ranar Asabar, 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 60 fansar yara 6 da suka sace a Abuja

Fasto ya haikewa matashiya
Yan Sanda Sun Kama Malamin Addini Bisa Zargin Haikewa Matashiya a Ogun Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda fasto ya turmushe matashiya a Ogun

Odutola ya ce sun karbi korafin wasu mazauna yankin Giwa Agbodo, a ofishin yan sanda dake Agbodo, biyo bayan yadda iyayen yarinyar suka ga sauyi a tattare da yar ta su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifan yarinyar sun ce sun shiga damuwa bayan da suka fuskanci yarinyar ta su tana cikin wani yanayi, kuma bayan da suka matsa lamba sai suka ci karo da cewa ta yi tarayya da namiji.

Bayan da suka matsa bincike ne sai yarinyar take basu labarin cewa Faston ne ya turmushe ta, kuma ya mayar da abin kamar aikin yau da gobe wajen mu’amala da ita tun daga watan Nuwamba na shekarar 2023.

Yarinyar ta kara da cewa Faston ya yi mata barazana da cewa zai illata ta idan har ta bayyanar da wannan sirrin dake tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka tisa keyar babban basarake a Najeriya

Jaridar Leadership ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ya ce:

“Yarinyar ta kuma gaya mana cewa Fasto yayi mata barzana da kisa, idan har ta shaida wa ko da iyayen ta ne cewa ga abinda ke tsakaninsu.”
“Lokacin da muke ci gaba da bincikar Faston, ya tabbatar mana da ya aikata wannan aiki na assha, kuma ya ce ya aikatawa yarinyar wannan aiki sau ba adadi.”
“Yarinyar da aka lalatawa rayuwar tata yanzu haka tana can wajen samun kulawar Likitoci, da kuma ci gaba da yi mata gwaje gwajen da suka kamata domin tabbatar da cewa kalau take."

Likita ya haikewa kanwar matarsa

A wani labarin kuma, mun ji cewa alkalin kotun Ikeja ya yankewa shugaban Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Optimal, Dr Olufemi Olaleye, hukunci a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba kan yi wa yar'uwar matarsa fyade.

Da yake zartar da hukunci, Maishari'a Rahman Oshodi ya bayyana cewa masu shigar da kara sun gamsar da kotun da hujjojin da suka tabbatar da cewa Olaleye ya aikata laifin, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: