An Yi Wa Matashi Tayin Naira Miliyan 80 Kan Wani Fili Ya Siya N250k a Shekarar 2000

An Yi Wa Matashi Tayin Naira Miliyan 80 Kan Wani Fili Ya Siya N250k a Shekarar 2000

  • Yan Najeriya sun fara ba wani mutumi shawara bayan ya bayyana wani tayi mai ban mamaki da aka yi masa kan filin mahaifinsa
  • A cewar matashi dan Najeriyan, mahaifinsa ya siya filin kan Naira dubu dari biyu da hamsin tun a shekarar 2000
  • Wannan bayani nasa ya haifar da cece-kuce, inda wasu suka shawarci mahaifinsa da kada ya siyar da shi kan wannan farashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya mai suna Joseph Okoro, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana cewa an yi masa tayin naira miliyan 80 a kan filin mahaifinsa.

Joseph ya ce mahaifinsa ya siya filin kan N250k a shekarar 2000.

An taya filin 250k kan miliyan 80
An Yi Wa Matashi Tayin Naira Miliyan 80 Kan Wani Fili Ya Siya N250k a Shekarar 2000 Hoto: Punnarong, Momo Productions
Asali: Getty Images

Ya bayyana cewa idan mutum ya yi hakuri, siyan fili a ajiye zai sauya rayuwar mutum. Rubutun nasa na Facebook ya zo kamar haka:

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jiya na samu wani tayi na N80m kan kadarar mahaifina da ya siya kan N250k a 2000.
"Idan ka yi hakuri siyan kadara ka ajiye zai sauya rayuwarka."

Kawunan yan Najeriya ya rabu wajen bayar da shawara kan ko mahaifi Joswph ya siyar da kadarar tasa ko kada ya siyar.

Jama'a sun yi martani

Miracle Onochie ya ce:

“Kada yarje ma kowa faaa, koda ka zabi siyarwa. Ke nemi wanda ya yi ciniki mafi tsada.
“Nan da shekaru uku masu zuwa mutane za su dunga taya wannan kadara kan miliyan 200.”

Nnamdi Matthew Nwedu ya ce:

"Babban kaya, idan mai saka jari ya taya 80M, wannan shine babban dalilin da zai sa na ajiye shi."

Nwachukwu Onyekachi said:

"Zan ba ka shawarar ka karba idan kana bukatar kudin sannan ka yi amfani da shi ka sayi wani wuri mai kyau daban.

Kara karanta wannan

Budurwa ta koka yayin da saurayi ya yasar da ita a filin jirgin sama, tana neman taimako

"Da naira miliyan 10, za ka iya samun wani wurin mai kyau."

Okeke Kenneth ya ce:

"Bara na je na tambayi mahaifina ko yana da fili don mutane su fara tayawa."

Matashi ya taya soyayyar budurwa N5m

A wani labari na daban, mun ji cewa soyayyar wata matashiyar budurwa yar Najeriya da sahibinta na shekaru bakwai ta hadu da tangarda.

A cewar wata mai amfani da dandalin X @dexterouz11, sahibinta ya hadu da wata sabuwar masoyiya don haka ya nemi su raba gari da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng