Dakarun Ƴan Sanda Sun Kama Mutane 2,931 Bisa Zargin Aikata Laifuka Fiye da 3 a Jihar Kano
- Hukumar yan sanda reshen jihar Kano ta bayyana nasarorin da dakarunta suka samu a faɗin kananan hukumomi 44 a 2023
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Hussaini Gumel, ya ce sun kama mutane sama da 2,500 bisa zargin aikata laifuka
- Ya ce sun magance matsalar ɓarayin waya da suka addabi mutane a Kano yayin da yan daba 662 suka tuba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama mutane 2,931 da ake zargi da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai da sauran laifuka a sassan jihar a 2023.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Hussaini Gumel ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Kano ranar Asabar, 6 ga watan Janairu.
CP Gumel ya ƙara da cewa dukkan waɗanda suka kama a shekarar da ta gabata sun gurfanar da su a gaban ƙuliya domin su girbi abinda suka shuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an aikata laifukan ne a kananan hukumomi 44 na jihar Kano, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Laifukan da ake zargin waɗanda aka kama sun aikata
A cewarsa, dakarun rundunar ƴan sandan sun kama mutane 337 da ake zargi da aikata laifin fashi da makami, da kuma wasu 55 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Kwamishinan ya ƙara da bayanin cewa sun kama mutane 65 bisa zargin dillalan miyagun kwayoyi ne, ɓarayin motoci 68, ɓarayin Keke Napep, ƴan damfara da ƴan daba.
A kalamansa, CP Gumel ya ce:
"Mun karɓi jimullar yan daba 662 da suka tuba, kana dakaru sun ceto mutane 25 da aka yi garkuwa da su da kuma 63 da suka shiga hannun masu safarar mutane a 2023."
Kwamishinan ya bayyana cewa, abubuwan da aka kwato a cikin shekarar sun hada da bindigogin AK guda hudu, bindigar Barretta daya, da sauransu.
Ya ce rundunar ta yi maganin barayin waya da suka addabi mazauna birnin Kano a kwanakin baya, cewar rahoton Pulse.
Ya kuma nemi goyon baya da hadin kai daga jama’a domin a ba su bayanan da za su taimaka wajen damke miyagu a tsakaninsu.
Kamfanonin jirage 3 zasu yi jigilar alhazan Najeriya
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta ware kamfanonin sufurin jiragen sama 3 da zasu yi aikin jigilar maniyya a aikin hajjin bana 2024.
Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ce ta sanar da sunayen tare da kamfanonin jiragen da zasu yi jigilar kayan alhazai.
Asali: Legit.ng