Yan Sanda Sun Kama Masu Shafin Tsegumi Na ‘Gistlover’, An Saki Hotunansu
- Rundunar yan sanda ta kama masu shahararren shafin nan na tsegumi mai suna 'Gistlover'
- A cewar wata sanarwa da rundunar yan sandan ta saki, an kama masu laifin ne kan zargin aikata manyan laifuka
- Kakakin yan sandan ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Rundunar yan sandan Najeriya mai yaki da laifuka ta Intanet, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hada kai da kuma barazana ga rayuwar wata, sakamakon korafin da wata mata mai suna Misis Seye Oladejo ta yi.
Wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta tabbatar da cafke Adebukola Kolapo mai shekaru 27, Nnedum Micheal Somtomchukwu mai shekaru 25 da Isaac Akpokighe mai shekaru 30.
Wadanda mutanen suna da alaka da wani shafin tsegumi da aka fi sani da suna Gistlover Family.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin mutanen uku da gudanar da shafin Gistlover, wani dandali na soshiyal midiya, kuma an garkame su bayan gudanar da bincike.
Kakakin rundunar yan sandan ya bayyana cewa, shafin ya yi kaurin suna wajen aikata ayyukan da suka hada da laifukan yanar gizo, tada zaune tsaye, da cin zarafi, da dai sauran laifuka daban-daban, lamarin da ya damu al'umma tsawon shekaru.
Sanarwar ta ce:
“Wanda ake tuhuma na farko Adebukola Kolapo wanda aka fi sani da Omo oba Gistlover ne ya bude sama da kashi 80 na shafukan Gistlover, inda ya ke sahun gaba wajen aikata laifin da aka ambata.
"Kasancewarsa cikin wadanda ake biya a shafin da samun kyaututtuka kamar su motoci da kudade, Adebukola shi ke da alhakin jiyo kwarmato, rubutawa da yi masu take, ciki harda rubutun da aka yi kan mai korafin, Dr Misis Oluseyi Oladejo.
“Adebukola ya kuma bayar da gudunmawa wajen wawure kudaden da aka samu daga haramtacciyar hanya ta hanyoyi daban-daban.
'Yan sanda za su gurfanar da wanda ake zargi
Bugu da kari, an gano Nnedum yana yada labarai, samar da maryani, da yin kalamai na batanci.
ACP Adejobi ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike, mutanen da abin ya shafa za su gurfana a gaban kotu.
An kama mutum 8 kan harin Filato
A wani labarin, mun ji cewa rundunar ƴan sanda reshen jihar Filato ta bayyana cewa ta kama mutum 8 da take zargin suna da hannu a kashe-kashen da aka yi kwanan nan a jihar Filato.
Rundunar ta ce dakarun ƴan sanda sun kama mutanen da ake zargin suna da alaka a kashe-kashen wanda aka yi a kauyukan kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi.
Asali: Legit.ng