Wasu Mata Sun Fito Zanga-Zanga a Fusace, Sun Banka Wa Gidan Basarake Wuta a Bokkos

Wasu Mata Sun Fito Zanga-Zanga a Fusace, Sun Banka Wa Gidan Basarake Wuta a Bokkos

  • Tashin hankali yayin da wasu mata da suka fito zanga-zanga suka banka wa gidan hakimin Bokkos wuta a jihar Filato
  • Bayanai sun nuna cewa matan sun yi haka ne domin nuna ɓacin ransu kan kama waɗanda ake zargi da kashe-kashen kwanan nan
  • Dakarun sojin Najeriya sun kai ɗauki wurin kuma an ce sun tarwatsa matan a halin yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Wasu gungun mata da suka fito zanga-zanga da tsakar rana yau Jumu'a sun ƙona gidan hakimin garin Bokkos, ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa matan sun banka wuta a gidan basaraken mai suna, Michal Monday Adanchi, da misalin ƙarfe 12:30 na rana.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun.
Plateau: Mata Sun Banka Wa Gidan Basarake Wuta a Karamar Hukumar Bokkos Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Majiyar ta ce matan sun kona gidan ne biyo bayan damke wasu mazauna yankin bisa zarginsu da hannu a kashe-kashen da aka yi a Bokkos kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta tattaro majiyar na ƙara bayanin cewa gidan basaraken da kuma ofishin da yake gudanar da harkokin shugabanci sun ƙone ƙurmus.

Majiyar ta ce:

"Lamarin dai ya fara ne a ofishin ‘yan sanda inda suka nuna bacin ransu bisa kame wasu daga cikin mazauna garin Bokkos.
"Bayan sun bar ofishin yan sanda sai suka wuce gidan basaraken, suka nuna ɓacin ransu cewa ya siyar da mutuncinsa. Suna zuwa gidan suka banka masa wuta."

Wane matakin jami'an tsaro suka ɗauka?

The Nation ta ruwaito cewa tuni dakarun rundunar Sojin Najeriya suka isa wurin kuma har sun tarwatsa matan da ke wannan zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wa ayarin 'yan kasuwa wuta, sun kashe mutane da yawa a jihar Katsina

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce zai kira DPO na yankin ta wayar tarho gabanin ya yi magana da ƴan jarida kan lamarin.

Rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Alhamis ta tabbatar da cafke wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a hare-haren baya bayan nan a kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi.

Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya a Abuja

A wani labarin kun ji cewa Yan bindiga sun kara zafafa kai hare-hare kauyukan da ke kewaye da ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya

Yan sanda biyu sun ji raunuka yayin da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai yan gida ɗaya a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262