"Gwanin Sha'awa" Hotunan Yadda Wata Gabjejiyar Budurwa Ta Rage Ƙiba Sun Girgiza Intanet
- Kokarin wata mata na rage ƙiba daga lokacin da aka mata tiyata zuwa shekaru uku bayan haka ya ƙayatar da mutane da dama a midiya
- Matar dai ta samu nasarar sauyawa daga mai ƙibar da ta wuce ƙima zuwa mace ƴar daidai sakamakom kokarin da ta yi
- Mutane da dama a manhajar X sun maida martani kan batun rage ƙiba inda suka riƙa bayyana wahalar da ake sha
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wata zankaɗeɗiyar mace ta bayyana yadda ta sha fama har ta yi nasarar rage ƙibarta wanda ya ja hankalin mutane a shafin sada zumunta X wanda aka fi sani da Twitter.
Jajirtacciyar matar, wadda ta tabbatar da cewa sai da aka mata tiyata, ta labartawa mabiyanta duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe.
A sakon da aka wallafa a manhajar X a shafin @oyindapenaddict, matar ta sake nanata cewa manufarta ita ce ta ƙara zaburar da wasu da ka iya fuskantar irin wannan kalubale.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mace mai jajircewa ta ɗage ƙiba, ta ƙayatar da wasu
Bayan shekaru uku tana kokarin bin matakan da aka zayyana mata, ƙatuwar matar ta rage ƙiba kuma an wallafa hotunan yadda ta dawo a soshiyal midiya.
Ta hanyar sadaukarwar da ta yi da kuma aiki tuƙuru, matar ta sami raguwar nauyi da ƙiba, ta canza kamanninta na zahiri da kuma yanayin tafiyar da rayuwa gaba ɗaya.
Yadda mutane suka jinjina mata a soshiyal midiya
Mutane da dama sun yi saurin yabawa canjin da ta samu ta rage kiba, tare da nanata kokari da sadaukarwa da ake bukata don cimma irin wannan gagarumin sakamako.
@ugo_hi ya yi raddi da cewa:
"Ya kamata wannan matar ta zama abin kwatance da kwarin guiwa ga sauran mata, da yawanku kuna bukatar ɗaukar darasi daga gare ta ku rage ƙiba, ku daina takura mana a Napep."
Ruth Is Favo ta ce:
"To ina ɗayan hoton wanda ya kamata a ce ya kiɗima ni?"
@MissKike ta ce:
"Wow gunin sha'awa, wannan aiki ba abu ne mai sauki ba."
Kamfanin Allura da Sirinji Ya Rufe Ofishinsa Na Najeriya
A wani rahotin kuma Kamfanin da ke kera Allura da sirinji a Najeriya ya dakatar da ayyukansa saboda taɓarɓarewar harkokin kasuwanci.
A wata takarda da ya aike wa ma'aikatansa, kamfanin ya ce ɗaukan wannan matakin ya zama tilas duba da halin da ya shiga.
Asali: Legit.ng