Kano: NDLEA Ta Kama Mutane Fiye Da 1,000 Kan Sha Da Fataucin Miyagun Kwaya

Kano: NDLEA Ta Kama Mutane Fiye Da 1,000 Kan Sha Da Fataucin Miyagun Kwaya

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce ta kwace akalla tan 9 na miyagun kwayoyi a shekarar 2023 a Kano
  • Hukumar ta kuma ce ta cafke sama da mutane 1000 da ake tuhuma da laifuka daban-daban masu alaka da miyagun kwayoyin
  • Hukumar ta ce za ta sake shiri don tabbatar da ta kakkabe duk wata kofa da za a yi ta'ammali da kwayoyi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce ta kama wadanda ake zargi da laifi aƙalla 1,016 tare da kwace tan tara na miyagun kwayoyi a Kano a shekarar 2023.

Babban kwamandan hukumar a jihar, Malam Abubakar Idris Ahmad, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano in da ya ce sun kama masu laifi mata 40 da maza 976.

Kara karanta wannan

Abba ko Gawuna? An hango wanda zai yi nasara a kotun koli duba da wasu dalilaia

Jami'an NDLEA
NDLEA reshen jihar Kano ta kama mutane sama da 1,000 kan laifukan sha da fataucin miyagun kwayoyi. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce hukumar ta tabbatar da laifin mutum 102 tare da izinin rike motoci biyar da kuma kararraki 104 da ke gaban kotu, rahoton The Punch.

An kwace wiwi, kodin, hodar iblis da wasu miyagun kwayoyi

Idris Ahmad ya ce an kwace kilo 6,098 na tabar wiwi, kilo 1,696 na kodin da tiramol da kuma kilo 1,335 na koken da methamphetamine.

"Mun nemawa mutane 70 lafiya, mun binciki izinin fita kasashen waje 598, mun kuma gudanar da gwajin kwayoyi guda 245, in da muka samu mutum shida da laifukan ta'ammali da kwayoyi daban-daban.
"Mun kuma ceto mutum 5,000 tare da dauko kwararru kan harkokin miyagun kwayoyi in da suka bai wa mutum 1,459 shawarwari," in ji Idris Ahmad.

NDLEA ta lalata tan 15 na magunguna masu dauke da sinadarin da ke gusar da hankali a Kano

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama dillali da ke sayarwa 'yan bindiga kwayoyi a Zamfara da Kebbi

Hukumar ta kuma lalata sama da tan 15 na magunguna masu dauke da sinadarin nikotin da kuma sinadarai masu gusar da hankali a 2023, a cewarsa.

Rahoton da The Guardian ta fitar na cewa ya kara jaddada aniyar hukumar wajen tabbatar da lafiya da tsaftace gari daga illolin shaye-shaye.

"Za mu sake zage dantse don kawar da shaye-shaye, mun kula da wanda ke bukatar kulawa, mu gurfanar da masu laifi, da kuma lalata duk wani abu mai sa maye da kuma dakile cinikin miyagun kwayoyi," Idris Ahmad ya bada tabbaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164