NDLEA Ta Kama Dillali Da Ke Sayarwa 'Yan Bindiga Kwayoyi a Zamfara Da Kebbi

NDLEA Ta Kama Dillali Da Ke Sayarwa 'Yan Bindiga Kwayoyi a Zamfara Da Kebbi

  • Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta yi nasarar kama wani dan kasuwan Najeriya mazaunin Qatar dauke da wasu ababe da ake zargin miyagun kwayoyi ne
  • Femi Babafemi, mai magana da yawun NDLEA ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Lahadi 31 ga watan Disamba yana mai cewa wanda ake zargin yana shirin ketarawa zuwa Doha
  • Har wa yau, jami'an na NDLEA sun yi wasu kame-kamen mutanen da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyin ne ciki har da wanda ya amsa cewa yana sayarwa yan bindiga kwaya a Zamfara da Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama Agu Amobi, wani dan kasuwa mazaunin Qatar, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, da ke Lagos, bisa zargin safarar kwayoyi.

Cewar sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Femi Babafemi, mai magana da yawun NDLEA, ya ce an kama wanda ake zargin ranar Asabar yayin da ya ke kokarin ketarewa zuwa Doha ta jirgin Qatar Airways.

Kara karanta wannan

Abba ko Gawuna? An hango wanda zai yi nasara a kotun koli duba da wasu dalilaia

NDLEA ta kama miyagun kwayoyi da dilallai masu kai wa yan bindiga kwaya
NDLEA ta kama wasu masu safarar miyagun kwaya ciki har da mai sayarwa yan bindigan Zamfara da Kebbi. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kama Amobi da kilo 1.30 na tabar wiwi da aka nade a jakar kayan abinci.

Ina safarar kwaya ne don biyan kudin haya da kudin makarantar yara - Amobi

Babafemi ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin a Qatar ya ke zaune sama da shekara 10 kuma ya na siyan kwayoyi daga Enugu ya kai Doha don ya samu ya biya kudin makarantar yaransa uku.

A wani makamancin rahoton a rana guda, Uchegbu Obi ya shiga hannu bayan an kama shi da kwayar tiramol da ta kai 72,000 a MMIA.

An ruwaito cewa Obi yayi kokarin aika kwayar daga Lagos zuwa Kano.

An kama mai yi wa 'yan bindiga safarar miyagun kwayoyi

Hukumar ta kuma tabbatar da kama mutum uku Musa Sani, Mohammed Ibrahim da kuma Adamu Usman da kurkura dauke da wiwi da nauyinta ya kai 15 da kuma kwaya har guda 128,500 a Jihar Yobe.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

Hukumar ta kuma wani mai shekaru 45 Yusuf Yahaya a jajeberin Kirismeti a hanyar Lagos zuwa Ibadan da kilo 31 na tabar wiwi a wata motar haya da ta taso daga Ibadan, jihar Oyo, zuwa Jihar Kebbi.

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun kwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun kwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164