DHQ: Duk da Kashe Bayin Allah 195, Sojoji Sun Dakile Munanan Hare-Hare a Garuruwa 19 a Filato

DHQ: Duk da Kashe Bayin Allah 195, Sojoji Sun Dakile Munanan Hare-Hare a Garuruwa 19 a Filato

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi ikirarin cewa duk da rasa rayuka 195, sun dakile hare-haren ƴan bindiga a kauyuka 19 a Filato
  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun fatattaki mahara a kauyukan ranar jajibirin kirsimeti
  • A cewar DHQ, matsalar hanya da rashin samun labarin kai harin ne ya hana sojoji kai ɗauki wasu kauyukan a kan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun dakile haren-haren da aka yi yunƙurin kai wa kauyuka 19 a jihar Filato a ranar 24 ga Disamba, 2023.

A jajibirin Kirsimeti, an tabbatar da mutuwar mutane 195 sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyuka a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe malami tare da sace bayin Allah sama da 35

Babban hafsan tsaro na kasa, CDS Christopher Musa.
DHQ: Dakarun Sojoji Sun Dakile Hare-Haren Yan Ta'adda a Kauyuka 19 a Jihar Filato Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Da yake jawabi ranar Juma’a a Abuja, Daraktan yada labarai na DHQ, Edward Buba, ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-hare ne a lokaci guda kan wasu kauyukan na daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba ya ce kai ɗaukin da sojojin suka yi a kananan hukumomin ya tilastawa wasu daga cikin maharan arcewa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kakakin DHQ ya ce sama da 'yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda ya kara da cewa sojojin sun samu kiran gaggawa daga wurare 36 daban-daban.

A rahoton Premium Times, Buba ya ce:

"Tazarar da ke tsakanin wasu kauyukan da inda sojoji suke ya haura kilomita 90 kuma akwai wahala kafin a kai saboda gargadar kan hanyar zuwa wasu kauyukan, galibi ba a iya shiga da motoci."
"Don haka wannan matsalar tana shafar kai ɗauki a kan lokaci in banda wuraren da aka samu sahihan bayanan leƙen asiri gabanin kai harin. Sojoji sun amsa kira sun shiga kauyaka 19 sun fatattaki maharan."

Kara karanta wannan

Bayan kashe bayin Allah 195 a jiha ɗaya, miyagu sun sake kai mummunan hari, sun tafka ɓarna

"Amma abin takaici, miyagun sun yi barna mai yawa kafin sojoji su isa sauran kauyukan.”

Idan baku manta a hare-haren jajibirin kirsimeti da aka kai kauyuka sama da 20 a Filato, mutane sama da 190 ne aka tabbatar sun mutu.

Yan bindiga sun shiga yankunan Abuja da Neja

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a birnin tarayya Abuja da jihar Neja da ke maƙotaka, sun kashe mutane huɗu.

Rahotanni sun nuna cewa yayin hare-haren a lokuta daban-daban, 'yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu mutane 39.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262