Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Shugaban ICAN Kuma Fitaccen Ɗan Kasuwa a Najeriya Ya Mutu
- Tsohon shugaban ICAN na ƙasa kuma fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya, Emmanuel Ijewere, ya riga mu gidan gaskiya
- Bayanai sun nuna cewa Mista Ijewere ya mutu ne ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023 bayan fama da dogon rashin lafiya
- Gabanin rasuwarsa ya riƙe manyan muƙamai da suka haɗa da shugaban babbar kungiyar noma ta Najeriya (NAGB)
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Emmanuel Ijewere, tsohon shugaban Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN), ya riga mu gidan gaskiya.
Dare Muyiwa, babban manajan sashin yaɗa labarai na ICAN, shi ne ya tabbatar da rasuwarsa ga jaridar The Cable a ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, 2023.
"Eh hakane Allah ya masa rasuwa," in ji Mista Muyiwa yayin da yake tabbatar da rasuwar tsohon shugaban ICAN a gajeren saƙo, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa Ijewere ya rasu ne jiya Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023 bayan kwashe tsawon lokaci yana jinyar rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa, Ijewere na ɗaya daga cikin fitattun 'yan kasuwa a Najeriya, yana da sha'awa da gogewa sosai a fannin harkokin banki, kuɗi, da noma.
Takaitaccen tarihin marigayin
Shi ne shugaban ICAN na 32, kuma ya jagoranci cibiyar daga 1996 zuwa 1997. Ya shugabanci manyan kungiyoyi kamar irin su Institute of Directors (IOD), da kuma Nigerian Red Cross.
An haife shi a shekarar 1946 kuma tsohon akantan ya yi karatu a jihar Legas, Ijebu-Ode, ƙasar Kamaru, da Ingila (Birtaniya).
Ya fara aikin akanta a shekarar 1965 inda ya yi aiki a kamfanin Coopers & Lybrand, daga bisani ya kafa kamfanin Ijewere & Co., mai kula da asusun ajiyar kudi a Najeriya a 1979.
Ya kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkar noma ga kwamitin mika mulki na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ijewere ya kasance shugaban kungiyar noma Agribusiness Group (NAGB), uwar kungiyar noma ta Najeriya, har zuwa rasuwarsa.
Iyalai sun yi magana kan mutuwar gwamnan Ondo
A wani rahoton na daban kuma Iyalan marigayi tsohon gwamna Oluwarotimi Akeredolu (SAN) sun nuna alhini yayin da suka tabbatar da rasuwar mai gidansu.
A cewar iyalan, marigayi Akeredolu ya rasu ne a cikin bacci yayin da yake ƙarƙashin kulawar likitoci kan cutar da ke damunsa a Jamus.
Asali: Legit.ng