IGP Ya Yi Kus-Kus da Gwamna Mutfwang, Ya Bada Muhimmin Umurni Yayin da Ake Kashe-Kashe a Filato

IGP Ya Yi Kus-Kus da Gwamna Mutfwang, Ya Bada Muhimmin Umurni Yayin da Ake Kashe-Kashe a Filato

  • Sufeto Janar na yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da wani sabon umurni don kwantar da tarzoma a jihar Filato
  • Ya bayar da umurnin ne jim kadan bayan ya isa garin Jos, babban birnin jihar Filato, don ganawa da Gwamna Caleb Mutfwang
  • A ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, IGP Egbetokun ya ba da umurnin tura tawaga ta musamman da kayan aiki jihar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jos, jihar Plateau - Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya isa garin Jos, babban birnin jihar Filato, don ganawa da Gwamna Caleb Mutfwang kan kisan kiyashin da aka yi wa daruruwan mazauna garuruwan Bokkos da Barkin-Ladi.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Mumunan al'amarin ya afku ne a ranar Kirsimeti, Litinin, 25 ga watan Disamba kuma tuni ya haifar da martani da dama daga dattawan kasa, masu sukar siyasa, kungiyoyin farar hula, da gwamnatocin jiha da ta tarayya.

IGP ya ziyarci jihar Filato
IGP Ya Yi Kus-Kus da Gwamna Mutfwang, Ya Bada Muhimmin Umurni Yayin da Ake Kashe-Kashe a Filato Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

A cewar Monday Kasa, shugaban kwamitin mika mulki a yankin Bokkos, an kai shiryayyun hare-haren tun daga ranar 23 ga watan Disamba zuwa jajiberin Kirsimeti, lamarin da ya kawo wa mazauna yankin cikas yayin shagalin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan rayuka da aka rasa na ta karuwa yayin da jami'an tsaro ke ta zagulo gawarwaki, kuma maharan, wadanda suka kona gidaje, sun kuma sace amfanin gona da lalata kayayyaki.

Sai dai kuma, Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da hargitsin, inda ya bukaci da a dauki matakin gaggawa, da kuma kara sanya idanu a yankunan da abun ya shafa.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da matar tsohon shugaban PDP da surukarsa suka mutu a jajiberin Kirsimeti

A halin yanzu, IGP Egbetokun, ya yi umurnin tura tawagar tsaro ta musamman da kayan aiki a ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba, sannan ya kuma bukaci AIG na Zone 4 ya gaggauta komawa jihar Filato.

Kwararre a harkar tsaro ya yi Allah-wadai da matakin da Egbetokun ya dauka

Ana tsaka da kashe-kashe masu tayar da hankali a Filato, kwararre a harkar tsaro Dr Abubakar Sani ya yi suka kan yadda yan sanda ke tafiyar da lamarin.

A wata hira da jaridar Legit, Dr. Sani ya jaddada muhimmancin magance matsalolin da ke tsakanin makiyayan da galibinsu Musulmi ne da kuma manoman Kirista.

Ya yi nuni da cewa basirar yan sanda da sa idonsu ba su yi daidai da halin da ake ciki ba, yana mai nuni ga muhimmancin daukar mataki da adalci kan lokaci.

UN ta magantu kan harin Filato

A wani labarin kuma, mun ji cewa majalisar dinkin duniya ta yi tir da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan jihar Filato a karshen shekarar nan.

Shugaban kula da hakkin bil adama a majalisar dinkin duniyan ya nuna hare-haren ya tada masa hankali, Daily Trust ta kawo rahoton

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng