Kamfanin Sufuri na Najeriya Ya Kaddamar da Adaidaita Mai Aiki da Gas da Fetur
- Wani kamfanin sufuri na Najeriya ya kaddamar da adaidaita sahu mai aiki da iskar gas da man fetur
- Kamfanin Egoras Technology ya ce ya kaddamar da ne daidaitar ne a madadin man fetur a Najeriya
- Kamfanin ya bayyana cewa 'yar kurkurar da ta samar na da fasahar gudanar da ayyuka daban-daban kuma tana da kwari fiye da wacce aka saba amfani da ita
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani kamfanin sufuri na Najeriya, mai suna Egoras Technology, ya kaddamar da adaidaita sahu mai aiki da iskar gas da fetur.
Shugaban kamfanin, Ugoji Harry, ya bayyana cewa an samar da adaidaita sahun ne domin magance matsalar da cire tallafin mai da aka yi a Najeriya ya haifar.
Adaidaita sahun na aiki da fetur da gas
Harry ya bayyana cewa yar kurkurar za ta kawo saukin kashe kudi ga mutanen birni da karkara, wanda zai bayar da gudunmawa ga tsaftar muhalli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce adaidaitar na aiki ne da fetur da kuma iskar gas, wanda hakan zai zama mafita ga masu amfani da ita.
Shugaban kamfanin na Egoras ya bayyana cewa baya ga amfani da fetur da gas, an kera yar kurkurar ne ta yadda masu tuka ta za su iya kula da ita cikin sauki.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Harry ya ce, adaidaitar wadda tuni aka watsa ta a wasu sassan kasar, ta yi fice a matsayin abar hawa mai karko da aminci.
Harry ya ce an yi wa adaidaitar gwaji sosai don tabbatar da amincinta da bin ka'idojin masana'antu, yana mai tabbatarwa masu amfani da ita da masu wucewa inganci da amincinta.
Ya bayyana cewa kamfanin na ci gaba da jajircewa wajen kawo sauye-sauye a harkar sufurin Najeriya, kuma cewa kaddamar da abar hawan wani muhimmin mataki ne na cikar buri.
Matashi ya kawata adaidaitarsa
A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a sun yi martani masu ban dariya bayan bayyanan bidiyon wani keken adaidaita sahu da aka kawata shi domin ya yi daban da saura.
Mai adaidaita sahun, @ortiz.1992, ya wallafa wasu jerin bidiyoyi a TikTok don nunawa mabiyansa abun hawan nasa.
Asali: Legit.ng