Ya Kamata Masu Kudin Najeriya Su Tallafawa Talakawa, Uwargidar Shugaban Kasa
- Matar shugaban kasa Bola Tinubu, Sanata Remi Tinubu, ta yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya gabannin shiga sabuwar shekara
- Oluremi ta roki masu hannu da shuni a kasar a kan su dunga taimakawa talakawa domin su ma su tashi a kan kafafunsu
- Uwargidar shugaban kasar ta kuma bukaci iyaye da su daina maganar talauci a gaban matasa domin yana kangarar da zukatansu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa ba za a iya bayyana Najeriya a matsayin matalauciyar kasa ba duk da halin da ake ciki, inda ta yi kira ga masu kudi da su taimakawa talakawa.
A sakonta na Kirsimeti bayan wani dan kwarya-kwaryan taron Kirsimeti da ta shiryawa yaran gidan marayu na Nana Berry da ke Abuja, Oluremi ta ce shekarar 2024 za ta zamo mai cike da alfahari ga yan Najeriya, rahoton Daily Trust.
Ku dunga karafafwa yara gwiwa su zama nagari, Uwargidar shugaban kasa ga iyaye
Har ila yau, uwargidar shugaban kasar ta shawarci iyaye da su ci gaba da karfafawa yaransu gwiwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce:
"Yayin da muke shiga shekarar 2024, ya kamata sakonmu ya zama kan yadda za a sauya rayuwar matasa. Ya kamata mu daina maganar talauci a gaban yaranmu, mu ba talakawa bane, ya kamata masu kudin cikinmu su kula da talakawa sannan su sa suma su zama masu arziki, shine abun bukata.
"Mun dauki lamarin talauci yadda bai kamata ba kuma yana gurbata zukatan matasa, amma ya zama dole mu karfafa masu gwiwa sannan mu nuna masu bangaren rayuwa mai dadi. Za mu shiga shekara mai haske kuma wadanda suka yarda cewa zai zama mai haske za su ji dadinsa."
Uwargidan shugaban kasar ta shawarci iyaye da su rungumi dabi’ar koyar da yaransu kyawawan dabi’u don su zama manya nagari, rahoton Punch.
Ta kuma shawarci iyaye da su fara koyar da yara ta hanyar Allah domin yara na da saurin fahimtar abubuwa.
Na yi kokari da Najeriya, IBB
A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya bayyana cewa babban nasarar da ya samu a matsayin jagoran Najeriya shine sanin kasar sosai da kuma yin abokai a fadin ko'ina.
Ya bayyana a wata hira ta musamman da gidan radiyo na jami'ar FUT Minna cewa zai shawarci matasan Najeriya da ke neman takarar shugabancin kasar da su nemi sanin mutanen ciki da fahimtar Najeriya sosai.
Asali: Legit.ng