PDP Ta Nemi EFCC Ta Ba Gwamnan Zamfara Hakuri Kan Wallafar da Ta Yi a Soshiyal Midiya

PDP Ta Nemi EFCC Ta Ba Gwamnan Zamfara Hakuri Kan Wallafar da Ta Yi a Soshiyal Midiya

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta bukaci hukumar EFCC da ta bayar da hakuri kan abun da ta bayyana a matsayin 'yada labaran karya'
  • An rahoto cewa EFCC ta yi wata wallafa a shafinta na Instagram wanda ke alakanta Gwamna Lawal Dare da Zamfara da badakatar tsohuwar minista, Diezani Alison-Madueke
  • Sai dai tuni hukumar yaki da rashawar ta goge rubutun da ya yi a shafinta na sada zumuntar Instagram a ranara Asabar, 23 ga watan Disamba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gusau, Zamfara - Jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ta nemi afuwa a kan wani rubutu da ta yi a Instagram wanda ke sako Gwamna Dauda Lawal a badakalar tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison-Madueke.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana yayin da alkaliyar Kotun Koli ta kira sanatoci da mijinta yayin tantance ta

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar EFCC ta cire labarin mai cike da takaddama wanda ya nakalto Diezani Allison-Madueke tana tattaunawa akan zargin karkatar da kudade da ake mata.

PDP ta nemi EFCC ta ba da hakuri kan Gwamna Lawal
PDP Ta Nemi EFCC Ta Bayar da Hakuri Kan Wallafar da Ta Yi Kan Gwamnan Zamfara a Soshiyal Midiya Hoto: Dauda Lawal Dare
Asali: Facebook

An goge wallafar, wanda ya yi ikirarin cewa tsohuwar ministar ta yi magana a wata hira da aka yi da ita a Birtaniya daga shafin EFCC na Instagram, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Koli ta wanke Gwamna Dauda tun a 2021 - PDP

A wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, sakataren labaran PDP a jihar, Alhaji Aliyu Bello Oando, ya bayyana cewa kotun kolin Najeriya ta wanke Gwamna Dauda Lawal daga zargin cin hanci da rashawa a ranar 12 ga Maris, 2021, rahoton Vanguard.

Alhaji Oando ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda EFCC ta yada labaran karya a dandalinta, yana mai jaddada cewa Kotun Koli ta yi watsi da karar da hukumar EFCC ta shigar kan Gwamna Dauda Lawal a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

Hakazalika ya ce kotun ta yi umurnin sakin N9,080,000,000.00 da hukumar yaki da rashawarar ta kwace daga wajensa.

Ya ce:

“Sauke labarin karyar bai wadatar ba. Yakamata hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar da sanarwa tare da gaggauta neman afuwa kan wannan abu da ke nuna rashin kwarewa a aiki."

Da farko Legit ta tuntubi wata majiya ta kusa da Gwamna Lawal don tabbatar da sahihancin zargin da aka bayyana a labarin da EFCC ta sauke.

Majiyar ta ce:

"Labarin karya ne da ake yadawa a shafin EFCC na Instagram, amma sun cire shi tun daga lokacin. Hakan ya fallasa makarkashiyar da ke tattare da shi. Za su nemi afuwa nan ba da jimawa ba."

Gwamnatin Zamfara ta kwato motoci 50

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ƙwato motoci kusan 50 da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi awon gaba da su.

Sani Sambo, mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, 7 ga watan Disamban 2023, cewar rahoton Channels tv.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng