Cikakkun Sunaye Sun Bayyana Yayin da Rundunar Soji Ta Samu Sabbin Janarori 112

Cikakkun Sunaye Sun Bayyana Yayin da Rundunar Soji Ta Samu Sabbin Janarori 112

  • A kwanan nan ne Majalisar Sojojin Najeriya ta kara wa wasu Birgediya Janar 47 girma zuwa Manjo Janar
  • Haka kuma, an karawa Kanar 75 girma zuwa mukamin Birgediya Janar kuma karin girman nasu ya biyo bayan yi wa janarori 113 ritaya a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba
  • Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, daraktan hulda na jama'a na rundunar soji ne ya tabbatar da ci gaban a wata sanarwa ga manema labarai

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani muhimmin mataki, Majalisar Sojojin Najeriya ta amince da yi wa wasu Birgediya Janar 47 karin girma zuwa mukamin Manjo Janar.

Bugu da kari, an daga darajar wasu Kanar 75 zuwa matsayin Birgediya Janar, wanda ke nuni ga wani gagarumin sauyi a rundunar soji.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane 52 a hannun 'yan bindiga yayin wani artabu, an bayyana matakin gaba

Rundunar soji ta samu sabbin janarori 112
Cikakkun Sunaye Sun Bayyana Yayin da Rundunar Soji Ta Samu Sabbin Janarori 112 Hoto: Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Wadannan karin girma da aka yi ya biyo bayan ritayar wasu manyan janarori 113 a farkon makon, wanda ya haifar da sabon shugabanci a cikin rundunar sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, wata sanarwa da Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya saki a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba, ya ce majalisar ta amince da karin girma ga manyan jami'ai a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.

Ya yi nuni da cewa, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukace su da su rubanya kokarinsu domin tabbatar da daukakar su da kuma kwarin gwiwa da ake da shi a kansu.

A cewarsa, wadanda aka karawa girma zuwa mukamin Manjo Janar sun hada da:

  1. Birgediya Janar WB Etuk
  2. Birgediya Janar JE Osifo
  3. Birgediya Janar WM Dangana
  4. Birgediya Janar TB Ugiagbe
  5. Birgediya Janar ASM Wase
  6. Birgediya Janar MA Abdullahi
  7. Birgediya Janar BI Alaya
  8. Birgediya Janar AO Oyelade
  9. Birgediya Janar OO Arogundade
  10. Birgediya Janar EI Okoro
  11. Birgediya Janar CR Nnebeife
  12. Birgediya Janar FU Mijinyawa

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da jami'in soja ya mutu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa

Sauran sune;

  1. Birgediya Janar MT Abdullahi Kwamanda 50 Space Command
  2. Birgediya Janar M Adamu
  3. Birgediya Janar ND Shagaya
  4. Birgediya Janar ME Onoja
  5. Birgediya Janar MO Erebulu

Wadanda suka kai matsayin Manjo Janar

  1. Birgediya Janar BA Ilori
  2. Birgediya Janar MO Ihanuwaze
  3. Birgediya Janar O Nwachukwu
  4. Birgediya Janar EE Ekpenyong
  5. Birgediya Janar SI Musa
  6. Birgediya Janar M Galadima
  7. Birgediya Janar AP Ahmadu

Jami'ai da suka kai matsayin Kanar

  1. Kanar Nwakonobi
  2. Kanar MC Akin Ojo
  3. Kanar BM Madaki
  4. Kanar MO Edide
  5. Kanar KE Inyang
  6. Kanar OO Nafiu
  7. Kanar PA Zipele
  8. Kanar OA Onasanya
  9. Kanar MI Amatso
  10. Kanar CM Akaliro
  11. Kanar NE Okoloagu
  12. Kanar AS Bugaje
  13. Kanar AM Kitchner
  14. Kanar SJ Dogo
  15. Kanar JN Garba

Hafsoshin da suka kai matsayin Birgediya Janar

  1. Kanar PT Gbor
  2. Kanar SO Okoigi
  3. Kanar AF Maimagani
  4. Kanar PO Alimekhena
  5. Kanar BI George
  6. Kanar IB Gambari
  7. Kanar AY Emekoma

Kara karanta wannan

An cafke matasa 5 kan mallakar bindigu a kauyen Katsina, yadda su ka samu makamin ya ba da mamaki

CDS ya magantu kan harin Tudun Biri

A wani labarin kuma, mun ji cewa babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da cewa rahoton binciken da aka yi kan harin bama-baman Kaduna zai fito nan ba da daɗewa ba.

CDS ya kuma ƙara tabbatarwa yan Najeriya cewa da zaran rahoton binciken ya kammalu, za a bayyana shi kowa ya san gaskiyar abin da ya faru a kauyen Tudun Biri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng