Gwamnan APC Ya Amince da Rabawa Ma’aikatan Jiharsa Kudi Mai Tsoka Don Bikin Kirsimeti
- Ma'aikatan gwamnati a jihar Ogun za su ji dadi iya son ransu a karshen shekarar nan sakamakon umurnin da Gwamna Dapo Abiodun ya bayar a baya-bayan nan
- Wata sanarwa daga gwamnatin jihar Ogun ta tabbatar da cewar Gwamna Abiodun ya amince da rabawa ma'aikata a dukkan matakai tagomashi
- Sanarwar ta tabbatar da cewar kudaden da za a rabawa ma'aikata zai kasance tsakanin N20,000 zuwa N100,000, ya danganta da matakin da mutum yake kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abeookuta, jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya amince da rabawa ma'aikatan gwamnatin jihar kyautar kudi na karshen shakara.
A cewar wara sanarwa da aka wallafa a shafin jihar na X a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, za a rabawa ma'aikata a dukkan matakai kyautar kudin ne domin rage masu radadin matsalolin da kasar ke ciki na tattalin arziki.
Kyautar kudin ya banbanta daga kaso 68 cikin dari zuwa kaso 159 na ainahin albashin da mutum ke kwasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Jami'ai a mataki na 01 za su samu kaso 159% mai ban sha'awa, yayin da sauran matakan za su samu kaso mabanbanta, bisa ga wata sanarwa daga ofishin shugaban ma'aikatan jihar (HoS).
"Jami'ai a mataki na 02 (165), mataki na 03 (135), mataki na 04 (122), mataki na 05 (113), mataki na 06 (104), mataki na 07 (88), mataki na 08 (81), mataki na 09 (88), mataki na 10 (70).
"Sauran sune mataki na 12 (80), mataki na 13 (80), mataki na 14 (68), mataki na 15 (70),mataki na 16 (102), sai mataki na 17 (84)."
Mataikatan Ogun a mataki na 16 da 17 za su samu kyautar 100k
A halin da ake ciki, kudin da za a bai wa yan mataki na 1-8 shine N20,000, mataki na 9 da 10 za su samu N25,000, mataki na 12 za su samu N35,000, mataki na 13 da 14 za su samu N40,000, mataki na 15 za su samu N55,000, sannan mataki na 16 da 17 za su samu N100,000.
Wannan shiri dai ya yi daidai da kokarin da gwamnatin Abiodun ke ci gaba da yi na tallafawa ma’aikatan gwamnati.
Haka kuma, a baya gwamnatin ta bai wa ma’aikatan gwamnati da suka hada da yan fansho da malamai alawus na kudin mota N10,000 saboda cire tallafin mai.
Gwamnan Ebonyi ya rabawa ma'aikata N100k
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya sanar da batun amincewa da N100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga daukacin ma'aikatan gwamnati a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, rahoton Nigerian Tribune.
Nwifuru ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki da dattawan jihar yayin kaddamar da aikin uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, wanda ya gudana a dakin taro da ke Abakaliki, rahoton Leadership.
Asali: Legit.ng