Gwamnatin Tunubu Zata Ƙara Tura Tallafin Kuɗi Ga Yan Najeriya Miliyan 4.5, Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin tarayya ta ce nan da ƙarshen shekara zata kara turawa yan Najeriya miliyan 4.5 tallafin N25,000 kowanen su
- Ministar jin ƙai da kawar da talauci, Doka Betta Edu, ta bayyana cewa kawo yanzun FG ta turawa mutum 3.5m tallafin
- Ta ce za a ƙara faɗaɗa tsarin wanda shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi alkawarin tallafawa magidanta 15m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta tura N25,000 ga ƴan Najeriya miliyan 3.5 kowanensu a tsarin tallafin marasa ƙarfi.
Ministan jin ƙai da kawar da talauci, Dokta Betta Edu, ce ta bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirinsu mai taken siyasa a yau ranar Alhamis.
Kalaman Edu na zuwa ne watanni biyu bayan Shugaba Tinubu ya kaddamar da tsarin wanda zai tallafawa magidanta 15m masu ƙaramin ƙarfi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasar ya tsara za a biya kowane mutum daga cikin wannan adadi N25,000 na tsawom watanni uku a wani yunƙuri na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
FG zata ƙara turawa yan Najeriya 4.5 tallafi
Da take karin haske kan inda aka kwana kawo yanzu, Betta Edu ta ce:
"Zuwa yanzu mun biya ‘yan Najeriya miliyan 3.5 Naira 25,000 kowanne. Muna kan aiikin zakulo wasu mutum miliyan 4.5 da zasu ci gajiyar wannan tallafi nan da mako ɗaya."
"Muna fatam daga nan zuwa ƙarshen shekarar nan ta 2023 zamu haɗa jimullar ƴan Najeriya Miliyan 8 da suka ci gajiyar N25,000 kowanen su."
A cewar Betta Edu, sai da ma'aikatar ta tantance dukkan waɗanda suka ci gajiyar tallafin a rukunin farko kuma yanzu haka tana kan matakin tantance wasu.
Ministar ta kara da cewa an kara faɗaɗa tsarin domin ya haɗa mutane da dama kamar ma'aikatan da suka yi ritaya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu daga cikin waɗanda suka samu tallafin a rukunin farko, kuma sun nuna farin cikinsu, wasu kuma sun fara sana'o'i.
Asiya Kabiru, ta gaya mana cewa ba ta yi tsammani ba kuɗin suka shiga asusunta kuma tuni ta fara sana'o'in mata domin dogaro da kanta.
Matar ta ce:
"Ni na san mun yi cike-cike a baya amma ban san taya na shiga tsarin ba, kawai Allah ya sa da rabona. Bayan na samu kuma gaskiya sana'a na fara irin tamu ta mata."
Wani magidanci, Aliyu Yusuf, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa wannan tallafi domin a cewarsa tabbas zasu rage wa duk wanda ya samu wasu harkokin.
Sai dai a cewarsa ya kamata gwamnati ta duba tsadar kayan abinci domin ita ce babbar matsalar da talakawa ke fama da ita.
Tsohon Gwamnan Arewa Ya Haddasa Sabon Rikici a Jam'iyyar PDP
A wani rahoton na daban Kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, kan rikicin jihar Ribas sun haddasa kace-nace a jam'iyyar PDP.
Yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta zargi Lamido da yi wa APC aiki, PDP ta Jigawa ta fito ta karyata ikirarin.
Asali: Legit.ng