Murna Yayin da Tinubu Ya Bayar da Sabon Umarni Kan Masu Cin Gajiyar N-Power
- Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a biya sama da mutum 400,000 da suka ci gajiyar N-Power kuɗaɗen alawus ɗin su
- Umurnin shugaban ya zo ne a ƙarshen aikin tantancewa da ma’aikatar jin kai ta gudanar kan masu cin gajiyar shirin
- An ce, umarnin na Tinubu, wanda aka samu a daren ranar Asabar, ya kawo farin ciki a tsakanin sama da mutum 400,000 da suka amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da masu cin gajiyar N-Power ke bi a faɗin ƙasar nan.
Umurnin Tinubu ya biyo bayan kammala wani aikin tantancewa da ma’aikatar jin ƙai da rage raɗaɗin talauci ta gwamnatin tarayya ta fara kuma ta kammala, inji rahoton The Cable.
Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya ba da umarnin biyan kuɗin N-Power
An ce an karɓi umarnin shugaban a daren Laraba, 20 ga watan Disamba, kuma ya jawo farin ciki ga sama da mutum 400,000 da suka amfana a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasheed Olanrewaju Zubair, mai baiwa ministan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 22 ga watan Disamba
Da take sanar da sakin kuɗaɗen, ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu, ta ce haƙiƙa wannan sabon fata ne ga matasan Najeriya domin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, rahoton The Punch ya tabbatar.
Minista ta yi magana kan biyan N-Power
Ministan ta yi nuni da cewa, nuna damuwar Shugaba Tinubu ga matasan Nijeriya ya tabbata ne saboda ɗimbin manufofi da tsare-tsare da gwamnatinsa ta ke da su musamman wajen ba su damammaki.
A kalamanta:
"Na kasance a farke tare da tawagar NPOWER har zuwa karfe 3:00 na dare a ofishin domin tabbatar da biyan waɗanda suka ci gajiyar NPOWER albashi kafin Kirsimeti kamar yadda shugaban ƙasa ya ba da umarni."
"Yanzu, zan iya tabbatar muku da cewa an fara biyan waɗanda suka ci gajiyar N-Power, kuma shaidun suna cikin asusun bankinsu."
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mai cin gajiyar shirin na N-Power, mai suna Ahmad Halilu, wanda ya tabbatar da cewa an fara biyan kuɗaɗen.
Ahmad ya yi nuni da cewa daga cikin kuɗin wata tara da suke bin bashi, na wata ɗaya kawai aka turo musu wato N30,000.
Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta cika alƙawarin da ta yi musu na biyansu dukkanin haƙƙoƙinsu.
An Faɗi Lokacin Biyan Basussukan N-Power
A baya rahoto ya zo cewa ministar jinƙai da yaƙi da fatara, Dr. Betta Edu, ta bayyana lokacin da za a biya basussukan masu cin gajiyar N-Power.
Ministar wacce ta ce har yanzu ana cigaba da bincike kan shirin, ta yi nuni da cewa ana sa ra fara biyan kuɗaɗen a watan Janairu.
Asali: Legit.ng