Bankuna Na Hada Baki da Masu Sana'ar PoS Don Hana Mutane Samun Wadatattun Takardun Naira, CBN

Bankuna Na Hada Baki da Masu Sana'ar PoS Don Hana Mutane Samun Wadatattun Takardun Naira, CBN

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi masu PoS da suke hana al'umma samun isasun takardun naira
  • Tana bincike kan korafe-korafen zargin kawo cikas ga tafiyar da tattalin arzikin kasa ba tare da matsala ba
  • Hakan ne zuwa ne bayan rahotannin cewa masu sana'ar PoS na caji fiye da 100% kafin bai wa mutane kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Babban Bankin Najeriya, (CBN) ya gargadi masu sana'ar PoS kan karancin takardun naira a fadin kasar.

An yi wannan gargadin ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Direktan Watsa Labarai da Hulda da Jama'a, Sidi Ali, a ranar Alhamis.

An gargadi masu PoS da bankuna
CBN ta yi zargin wasu bankuna da masu PoS na hada baki. Hoto: CBN
Asali: UGC

CBN ya ce akwai hadin baki tsakain wasu bankuna da ake ajiyar kudi da masu sana'ar biyan kudi na PoS don kawo cikas wurin wadutuwar takardun naira a kasar, rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Babban labari: Bankin CBN ya janye dokar da ya kakabawa masu kasuwancin 'Cryptocurrency' a Najeriya

Za a hukunta bankuna da masu sana'ar PoS

Babban Bankin na Kasa ya gargadi bangarorin biyu su dena aikata hakan nan take ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Sanarwa ta ce:

"An janyo hankalin Babban Bankin Najeriya (CBN) kan abin da aka kira hadin baki tsakanin wasu Bankunan Ajiyar Kudade da masu sana'ar PoS da haka ke kawo cikas wurin wadatar da al'umma da naira."

Ta kuma ce tana binciken korafe-korafen da aka shigar da ka iya kawo cikas ga tafiyar da tattalin arziki.

Martanin babban bankin na zuwa ne bayan mutane a kasa sun koka kan cewa har yanzu ba su samun isasun takardun naira yayin da masu PoS ke amfani da damar don zaluntar kwastomominsu.

CBN ya kuma shawarci yan Najeriya su rika amfani da wasu kafafen kuma su rika shigar da korafinsu ta kafar intanet da aka bada a sanarwar.

Legit.ng ta rahoto cewa masu sana'ar PoS sun yi ikirarin cewa ma'aikatan banki ne cewa su biya N10,000 kan kowanne N100,000 da za su karba a banki.

Kara karanta wannan

An bankado manyan abubuwa 2 da suka jawo karancin takardun naira a hannun 'yan Najeriya

Bincike ya nuna cewa bankunan kasuwanci sun kayyade cire tsabar kudi a cikin banki zuwa N20,000 da N50,000.

A na'uarar ATM kuwa, bankunan sun takaita kudin da za a iya cirewa zuwa N50000 mai maimakon N100,000 da ake iya cirewa a baya.

CBN Ya Aika da Sabon Umarni Ga Bankuna Game Da Amfani da Tsaffi da Sabbin Naira

A wani rahoton, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci rassansa na fadin kasar nan su ci gaba da mu'amala da tsaffi da sabbin takardun naira.

CBN ya umarci su bayar tare da karban dukkan takardun naira, tsaffi da sabbi, yayin gudanar da harkoki da Bankunan Kasuwanci (DMBs).

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164