Shugaba Bola Tinubu Ya Dira Jihar Legas, An Bayyana Muhimmin Abinda Zai Yi

Shugaba Bola Tinubu Ya Dira Jihar Legas, An Bayyana Muhimmin Abinda Zai Yi

  • Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Legas tare da hadimansa domin yin hutun bikin kirsimeti mai zuwa a mako na gaba
  • Gwamna Babajide Sanwo-olu da mataimakin gwamnan Legas, Obafemi Hamzat, ne suka tarbi mai girma shugaban kasa
  • Tinubu ya dira a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da ƙasa na Murtala Muhammad da ke Ikeja da misalin karfe 3:50 na ranar Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dira a jihar Legas yau Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023 domin yin hutun kirsimeti a gida.

Shugaban Ƙasar ya isa jiharsa ne a wani jirgin sama mallakin rundunar sojin saman Najeriya tare da hadimansa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Dira Jihar Legas Domin Yin Hutun Kirsimeti a Gida Hoto: NGRPresident
Asali: Twitter

Fadar shugaban ƙasa ce ta tabbatar da haka a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a can baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin da ke ɗauke da Shugaba Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya sauka ne a ɓangaren shugaban kasa da ke filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad a Ikeja.

Bayanai sun nuna cewa jirgin ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 3:50 na yammacin ranar Alhamis, sannan shugaba Tinubu ya fito daga ciki bayan minti 10.

Gwamnan Legas ya tarbi shugaba Tinubu

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya tarbi shugaban kasar tare da mataimakin gwamnan jihar, Obafemi Hamzat, da kuma hukumomin tsaro.

Jim kaɗan bayan fitowarsa daga cikin jirgin, Shugaba Tinubu ya zarce kai tsaye zuwa barikin Dodan.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

Wannan na zuwa ne awanni kalilan bayan Shugaba Tinubu ya sanar da rage farashin sufuri daga wasu jihohi da zuwa wasu wurare da kaso 50.

Ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa ma'aikata da sauran ƴan Najeriya da ke haramar komawa gida domin yin bukukuwan kirsimeti a mako mai zuwa.

Rikicin siyasa ya ɓalle a APC ta jihar Benuwai

A wani rahoton kuma Rigima na neman ɓallewa tsakanin ƴan majalisun tarayya na APC da Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai

Tawagar ƴan majalisun APC da suka fito daga Benuwai sun caccaki Gwamna Alia da gudanar da mulkin kama karya mara tsari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262