Hukumar JAMB Ta Kara Kudin Jarabawar UTME Ta 2024? Gaskiya Ta Bayyana
- Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a (JAMB) ta yi magana kan ƙarin kuɗin jarabawar UTME ta 2024 da aka ce ta yi
- Shugaban hukumar a yayin da ya bayyana a gaban kwamitin ilmi na majalisar wakilai, ya ce hukumar ba ta ƙara kuɗin jarabawar ba
- Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa kuɗin da aka ƙara na masu gudanar da cibiyoyin CBT wanda hukumar za ta riƙa biya kai tsaye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB), Farfesa Is-haq Oloyede, ya yi ƙarin haske kan ƙarin kuɗin jarabawar UTME.
Oloyede ya ce ƙarin kuɗin wani caji ne da masu gudanar da cibiyoyin ƙwamfuta domin zana jarabawar (CBT) suka yi saboda tsadar man fetur, cewar rahoton Daily Trust.
Domin haka ya musanta cewa hukumar jarabawar ta kara kuɗin jarabawar na shekarar 2024, rahoton The Nation ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin ilimi a zauren majalisar a ranar Laraba.
A cewarsa, hukumar ta JAMB ta sauƙaƙa hanyoyin karɓar kudaden ne kawai ta yadda masu cibiyoyin gudanar da jarabawar ba za su tatsi ɗaliban sosai ba.
Shin da gaske JAMB ta ƙara kuɗin jarabawar UTME?
A kalamansa:
"Kuɗaɗen ba JAMB ba ce ke biya amma ɗaliban ne ke biya da kansu. Kun san cewa N700 kuɗin rajista da N700 domin kuɗin jarabawa, amma saboda kuɗin dizal a wannan shekarar sai muka bar su yi ƙari."
"Wannan shekarar muna shirin fitar sanarwa. Sanarwar hakan ba ta daɗe da fitowa ba. Za mu bar su karɓi har N1500 domin UTME saboda ƙarin kuɗin man dizal."
"Amma kun gani daga manema labarai a cikin makon da ya gabata cewa JAMB ta kara kuɗin jarabawa. Abin da muka yi shi ne ƙyale cibiyoyin CBT su karɓi fiye da abin da su ke karɓa."
"Amma mu zamu karɓar musu, meyasa zamu karɓar musu? Saboda idan muka ƙyale su za su tatsi ɗaliban sosai, inda za su riƙa karɓar N4000 ko N5000. Shiyasa muka ce ɗaliban su biya ta hannun mu sai mu tura musu duk mako."
Ilmi Na Fuskantar Barazana a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana ƙarin kuɗin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) a matsayin babbar barazana ga ilmi a Najeriya.
Sanusi Yau Mani, wakilin ɗaliban Durbin Mani ya bayyana hakan inda ya ce za a ƙara samun yawaitar zauna gari banza saboda karin kuɗin jarabawar.
Asali: Legit.ng