Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Wani Matashin Ango Ya Mutu Kwana Uku Kafin Ɗaura Aurensa
- Abokanai sun shiga jimami yayin da abokinsu da ke shirin zama ango ya rasu kwana uku kafin ranar ɗaura aure
- Rahotanni sun nuna Abraham Basif ya kwanta dama yayin da ake shirin aurensa ranar Jumu'a da Asabar mai zuwa
- Ɗaya daga cikin abokansa, Theophilus Baba, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na dandalin sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wani Ango mai jiran gado wanda ya rage saura kwanaki uku a ɗaura masa aure, Abraham Basif, ya riga mu gidan gaskiya.
Abokan angon sun shiga jimami da kaɗuwa yayin da suka samu labarin rasuwar awanni 72 kaɗai gabanin a ɗaura masa aure.
Wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook, Theophilus Baba, ne ya tabbatar da rasuwar Abraham Basif, a shafinsa ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya wallafa hoton marigayin a shafinsa, Baba ya ce:
"Mutuwar matashi mai tasowa da buri tana sa ni kaɗuwa a cikin jikina matuƙa amma Allah ne ya san komai. Ban taba tunanin ranar da na zo gaishe ka a asibiti ita ce ranar haɗuwarmu ta karshe a duniya ba ɗan uwa."
"Kamata ya yi a ce zuwa ranar Jumu'a da Asabar zan zo ina rubuta kalaman murna da farin ciki a kan hotonka amma duk hukuncin da Allah ya yanke daidai ne."
Yaushe ne ranar ɗaura auren?
Yayin da muka duba shafin Facebook na Basif Abraham, mun ga cewa abu na ƙarshe da ya wallafa a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2023 shi ne katin gayyata.
Ya sa katin gayyatar yan uwa da abokan arziƙi zuwa wajen ɗaura aurensa da za a yi ranar Jumu'a 22 da Asabar 23 ga watan Disamba.
Yadda mutane suka yi jimamin rasuwar
Bayan sanarwar Baba, sauran abokan marigayin suma sun yi jimamin rasuwar Basif a shafukansu na Facebook.
Suleiman Naphysah ya rubuta cewa, “Na gaza yarda da labarin nan. Wannan yana da wuyar jurewa ga duk wanda ya san ka. Allah ya sa ka huta, Abraham Basif."
Voiceman Austine ya ce, “Ka huta lafiya, ɗan’uwa. Yanzu me zai faru da aurenku jibi, yallabai?"
Majalisa ta janye shirin tsige Fubara
A wani rahoton kuma kun ji cewa majalisar dokokin jihar Ribas ta janye shirinta na tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan samun maslaha a zaman da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya jagoranta a Villa
Asali: Legit.ng