Yan Bindiga Sun Sace Mai Shari'a Da Direbanta Bayan Kashe Dan Sanda Mai Tsaronta
- Yan bindiga sun sace alkaliyar babban kotu a karamar hukumar Oron na jihar Akwa Ibom, Mai shari'a Joy Uwanna, da direbanta
- Dan sanda mai tsaron Mai Shari'a Uwanna ya rasa ransa yayin harin na daren ranar Litinin, 18 ga watan Disambar 2023
- Shugaban kungiyar lauyoyi na Najeriya, reshen Oron, Torosco Eyene, ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin a ranar Talata 19 ga watan Disamba
Akwa Ibom - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace alkalin Babban Kotun Jihar Akwa Ibom, Mai Shari'a Joy Uwanna da direbanta, tare da kashe dan sanda mai tsaronta.
An tattaro cewa yan bindigan sun yi shiga ce irinta yan banga a hanyar Uyo-Okobo a daren ranar Lahadi, kuma suka tare hanyar suka hana Mai Shari'a Uwanna wucewa daga hanyarta daga zaman kotu a Oron, The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa yan bindigan sun bude wuta suka kashe dan sandan da ke tsaron alkaliyar. Sai kuma suka yi awon gaba da alkaliyar da direbanta, suka bar gawar dan sandan.
Shugaban Kungiyar Alkalai reshen Oron ya tabbatar da afkuwar lamarin
Torosco Eyene, ciyaman din kungiyar lauyoyi na kasa reshen garin Oron, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata a Uyo, ya ce an sace alkaliyar kan hanyar Okobo a hanyarta na komawa Uyo bayan zaman kotu, rahoton Daily Trust.
Eyene ya ce mambobin kungiyar ta NBA za su gana da kwamishinan yan sanda da shugaban hukumar yan sandan farin kaya a gobe (Laraba).
"Eh, an sace alkaliyar a Oron jiya (Litinin) a hanyarta na komawa Uyo bayan zaman kotu. Gobe, Laraba, za mu tafi Uyo don ganawa da kwamishinan yan sanda Olatoye Durusinmi da DSS kan lamarin," in ji shi.
Martanin yan sanda kan sace alkaliyar
Da aka tuntube kakakin yan sandan, Akwa Ibom, SP Odiko Macdon, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa kwamishina ya bada umurnin a gudanar da sahihin bincike kan lamarin.
"Abin takaici ne cewa an sace alkaliya da ke aiki a babban kotu. Rundunar, karkashin CP Olatoye Durosinmi ya bada umurnin yin sahihin bincike. A yanzu, ba za a yi kasa a gwiwa ba, za a yi duk mai yiwuwa don ganin an sada alkaliya da iyalanta.
"Na yi magana da iyalan dan sandan da ya mutu, wanda kafin rasuwarsa shine mai tsaron alkaliyar. Za a yi adalci kuma za a hukunta wadanda suka aikata laifin," a cewarsa.
Asali: Legit.ng