Karin Bayani: Gwamnan Arewa Ya Sa Labule da Babban Hafsan Tsaro Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu 1
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai na ganawar sirri yanzu haka da babban hafsan tsaro na kasa a birnin tarayya Abuja
- Gwamnan ya isa hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) da misalin karfe 1:19 na tsakar rana yau Talata, 19 ga watan Disamba tare da muƙarrabansa
- Duk da ba a bayyana makasudin wannan ganawa ba, wani hadimin gwamna Alia ya ce zasu tattauna ne kan batun tsaro a Benue lokacin kirsimeti
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnan jihar Benuwai da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya, Hyacinth Alia, ya sa labule yanzu haka da babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa.
Har kawo yanzu ba a bayyana maƙasudin wannan taro ba kuma babu wata sanarwa da ta yi bayanin batutuwan da manyan jiga-jigan biyu za su tattauna.
Amma ɗaya daga cikin hadiman Gwamna Alia ya shaida wa jaridar Daily Trust bisa sharaɗin ɓoye bayanansa cewa taron zai maida hankali ne kan yanayin tsaro a Benuwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene makasudin wannan ganawa?
A cewarsa, Gwamnan da CDS Musa zasu tattauna ne kan samar da ingantaccen tsaro yayin bukuwawan kirsimeti da ke tafe a jihar.
Gwamna Alia ya dira hedkwatar tsaro ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja da misalin ƙarfe 1:19 na tsakar rana yau Talata, 19 ga watan Disamba, 2023.
Haka nan kuma gwamnan na tare da jami'an gwamnatinsa ta jihar Benuwai, waɗanda suka raka shi zuwa DHQ domin ganawa da babbak hafsan tsaron.
Jihar Benuwai na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Tsakiya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga da ake zaton fulani makiyaya ne.
A mako mai zuwa ne mabiya addinin kirista a Najeriya da sauran kasashen duniya zasu gudanar da bukukuwan kirsimeti, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
CDS ya yi magana kan binciken harin bam a Kaduna
A wani rahoton na daban CDS Christopher Musa ya bayyana inda aka kwana a bincike kan harin bama-baman da sojoji suka kai a taron Musulmi a Kaduna.
Babban hafsan tsaron ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sakamkon binciken domin kowa ya san abin da ya faru.
Asali: Legit.ng