Gwamna Bago Ya Hana Ma’aikata Sanya Babban Riga da Kaftani? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamnan Neja, Umar Bago ya yi karin haske kan batun hana ma'aikatan gwamnati sanya babbanriga da kaftani zuwa wajen aiki a jihar
- Bago ya ce magauta ne suka yanke bidiyonsa da ke magana kan wannan batu tare da yada shi don bata masa suna
- A cewarsa, ya dai shawarci ma'aikatan gwamnati da su rungumi harkar noma saboda yadda gwamnatinsa ta zuba jari a bangaren
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Niger - Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa bai umurci ma'aikatan gwamnati a jihar su daina sanya tufafin gargajiya da suka hada da babbanriga da kaftani zuwa ofis ba.
Gwamnan na Neja ya ce an yi wa kalamansa kan yanayin shigar ma'aikata gurguwar fahimta ne, rahoton The Cable.
Magauta ne suka yanke bidiyon don bata mani suna, Bago
A ranar Litinin, 18 ga watan Disamba ne dai aka nakalto Bago yana cewa dole a daina sanya kayan gargajiya kamar su Kaftani da Babbanriga zuwa ofis daga Litinin zuwa Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya saki a daren Litinin, Bologi Ibrahim, babban sakataren labaran gwamnan, ya ce kawai dai Bago ya ba ma'aikatan gwamnati shawarar zama manoma ne sannan cewa manyan manoma kan yi shiga ta alfarma zuwa wajen aiki.
Ibrahim ya ce an yi wa kalaman gwamnan da ke kunshe a bidiyon da ya yadu kwaskwarima ne don bata masa suna, rahoton The Guardian.
Ya ce:
"Mai girma gwamna ya yarda cewa babu dalilin kasancewa cikin talauci saboda yawan noma da jihar ke yi.
"Tuni gwamnatinsa ta saka hannun jari sosai a bangaren noma. Don haka akwai bukatar a hadu a rungumi harkar noma - ciki harda ma'aikatan gwamnati.
"Kawai dai gwamnan yana karfafawa ma'aikatan gwamnati gwiwar zama manoma ne sannan kuma kafin mutum ya zama babban manomi, kana bukatar yin shiga mai kyau zuwa gona.
"Babu ta inda jawabin gwamnan ya nuna cewa yanzu ma'aikata na da irin tufafin da za su dunga sanyawa zuwa ofis daga Litinin zuwa Alhamis kamar yadda aka dauko a bidiyon da ke yawo."
Legit Hausa ta zanta da wata ma’aikaciyar gwamnatin jihar Neja don jin ta bakinta kan sabon matsayin gwamnan.
Malama Sa’adatu ta ce ta ji dadi sosai ta samu labarin cewa gwamnan ya nesanta kansa daga batun daina sanya tufafin gargajiya ta ce:
“Alhamdulillah na ji dadi sosai da na samu labarin cewa gwamnanmu Bago ya karyata batun hana ma’aikata sanya tufafinmu na al'ada.
Da farko bayan na samu labarin na shiga zullumi musamman ganin cewa wai ya yi barazanar sallamar duk wanda ya take dokar daga aiki. Cikinmu akwai matan aure ta yaya za mu fara sanya kaya yan kanti da ke bayyana sura zuwa wajen aiki? Muna fatan gwamnan zai tsaya kan matsayinsa na janye wannan umurnin. Nagode.”
Matsayin gwamnan Ondo kan tufafin gargajiya
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa gwamnatin jihar Ondo karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu ta umurci dalibai a makarantun kudi da na gwamnati da su koma sa kayan gargajiya duk ranar Jama’a.
Legit.ng ta tattaro cewa wannan shine matsaya da aka cimma yayin wani taro na majalisar zartarwa a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng