Tashin Hankali Yayin da Wasu Tsageru Suka Kai Hari Hukumar Gwamnati a Abuja, Bayanai Sun Fito

Tashin Hankali Yayin da Wasu Tsageru Suka Kai Hari Hukumar Gwamnati a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Jami'an ma'aikatar birnin Abuja (FCTA) sun damƙe wasu tsageru bisa kai hari hukumar gudanarwa na birni ranar Litinin
  • Waɗanda aka kama sun mamaye harabar hukumar da ke Wuse ne domin nuna fushi kan rushe musu gine-gine a wata Anguwa
  • Daraktan hukumar ya bayyana cewa suna cikin taro masu zanga-zangar suka shigo suka ɗaga masu hankula

FCT Abuja - Jami'an tsaron haɗin guiwa na ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) sun kama wasu miyagun yan daba 19 yayin da suka fita sintirin tsaftace gari.

Jami'an sun kama waɗanda ake zargin ne bisa kai hari hukumar gudanarwa ta kwaryar birnin Abuja (AMMC) da ke Wuse a Abuja ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Yan Daba Sun Farmaki Wata Babbar Ma'aikata a Birnin Tarayya Abuja Hoto: Nyesom Wike, FCTA
Asali: Facebook

Ƴan daban sun mamaye hukumar ne da sanyin safiyar ranar Litinin kan rushe wasu gine-gine a Mechanic Village da ke Kubwa, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa CDS zai tona asirin wasu jiga-jigan masu laifi a Najeriya

Jami'an hukumar AMMC ne suka yi rusau a Anguwar lamarin da ya fusata matasan suka mamaye hukumar da safiyar ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kama masu zanga-zangar?

Darakta a AMMC, Mukhtar Galadima ya shaidawa ƴan jarida bayan faruwar lamarin cewa, ma’aikata na cikin gudanar da aikinsu sa'ilin da ‘yan daban suka mamaye su.

Galadima ya ce an kama mutane 19 daga cikin masu zanga-zangar ne da laifin kawo cikas ga zaman lafiya a yankin.

Ya ce:

"Muna tsaka da taro sai muka ji hayaniya, muka fito mu ga meke faruwa sai muka ci karo da wasu mutane ɗauke da allunan zanga-zanga."
"Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna ƙorafi ne game da yankin Makanikai na Kubwa inda suka mallaki shaguna a wurin amma hukumar kula da ci gaba ta rusa su."

Meyasa hukumar ta rusa wurin?

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta tsare matasa 4 kan shaye-shaye da buga ludo a cikin masallaci, sun yi martani

Galadima ya bayyana cewa waɗanda suka ɗauki nauyin zanga-zangar sun je bisa son ransu suka gina abinda suka kira "Mechanic Village" a cikin kadarar wani.

Ya ƙara da cewa bisa haka hukumar ta umarci a rushe wurin gaba ɗaya saboda ba na su bane, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tinubu ya sa labule da tawagar wakilan NPAN

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu na ganawa da wakilan kungiyar gidajen jaridu ta ƙasa (NPAN) a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban kamfanin jaridar Daily Trust kuma shugaban NPAN na ƙasa, Malam Kabiru Yusuf, ne ya jagoranci tawagar zuwa Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262