Yanzun nan: Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wakilan NPAN Ta Ƙasa a Villa, Bayanai Sun Fito

Yanzun nan: Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wakilan NPAN Ta Ƙasa a Villa, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu na ganawa da wakilan kungiyar gidajen jaridu ta ƙasa (NPAN) a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
  • Shugaban kamfanin jaridar Daily Trust kuma shugaban NPAN na ƙasa, Malam Kabiru Yusuf, ne ya jagoranci tawagar zuwa Villa
  • Wannan ne karo na farko da shugaban ƙasa ya gana da kungiyar NPAN tun da ya karbi ragamar mulkin Najeriya a watan Mayu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa yanzu haka da wakilan ƙungiyar gidajen jaridu ta ƙasa (NPAN) a Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban NPAN kuma shugaban kamfanin Media Trust na jaridar Daily Trust da Trust Television, Mallam Kabiru Yusuf, ne ya jagoranci tawagar zuwa fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara tunanin ɗauko tsohon ministan Buhari ya maye gurbin Lalong, ya gana da jiga-jigai 2

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Yanzun nan: Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wakilan NPAN Ta Ƙasa a Villa, Bayanai Sun Fito Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa yanzu haka Bola Tinubu da tawagar wakilan kungiyar sun sa labule a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yau Litinin, 18 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin waɗanda suka halarci ganawa da Tinubu a Villa

Tawagar wakilan NPAN da suka shiga ganawa da Tinubu sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Ogun, Chief Segun Osoba; shugaban kamfanin jaridar Vanguard, Uncle Sam Amuka, da shugaban Thisday, Prince Nduka Obaigbena.

Sauran wakilan sun kunshi babban daraktan kamfanin jaridar The Nation, Victor Ifijeh, mataimakin shugaban jaridar Leadership, Azubuike Ishiekwene; da manajan darakta na Thisday, Eniola Bello.

Sai kuma manajan darakta na kamfanin jaridun Businessday, Frank Aigbogun; manajan darakta na kamfanin jaridun New Telegraph, Ayodele Aminu da kuma sakataren NPAN na ƙasa, Feyi Smith.

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan ne karo na farko da Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin kungiyar NPAN tun da ya ɗare kan kujera lamba ɗaya a Najeriya a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki mataki bayan babban minista ya yi murabus

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci kan zaɓen yan majalisa 4

A wani rahoton Jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato ta mayar da martani kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara game da zaben yan majalisar wakilai huɗu

A wata sanarwa, PDP ta nuna farin ciki bisa yadda ƴan takararta suka samu nasara, tana mai cewa abinda mutane suka zaɓa ne ya tabbata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262