Bayan Tinubu Ya Tsige Shi, Tsohon Shugaban NSIB Ya Tona Gaskiyar Abinda Ya Faru a Aikinsa

Bayan Tinubu Ya Tsige Shi, Tsohon Shugaban NSIB Ya Tona Gaskiyar Abinda Ya Faru a Aikinsa

  • Tsohon shugaban hukumar NSIB da aka tsige ya bayyana yadda ya aurensa ya rushe da wahalar da ya sha saboda kokarin yin gaskiya a bakin aiki
  • Injiniya Akin Olateru, wanda tun 2017 yake kan kujerar, ya ce ba ya kishi da sabon wanda zai gaje shi saboda aikin ba ƙarami bane
  • Ya kuma roƙi ma'aikatan hukumar afuwa waɗanda wataƙila ya musu ba daidai ba saboda son ran da wasu suka ziga shi a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon Darakta Janar na Hukumar kiyaye Haɗurran Jirage ta Najeriya (NSIB), Injiniya Akin Olateru, a ranar Litinin ya ce ya rasa aurensa yayin gudanar da aikinsa.

Ya ce aikin na da matukar wahala, inda ya ce baya kishi ko hassada ga sabon mutumin da aka naɗa zai gaje shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An bankado wata kullalliya da gwamnatin Tinubu take yi wa Peter Obi

Shugaban NISB da ya sauka, Akin Olateru.
"Na Rasa Aure Na, Ina Samun Barazanar Kisa Yayin Gudanar da Aiki, Tsohon Shugaban NSIB Hoto: Nigerians Safety Investigation Bureau
Asali: Facebook

Olateru ya yi wannan furucin ne a wurin wani ɗan gajeren bikin mika ragamar mulki ga sabon shugaban hukumar NSIB, Mista Alex Badeh, jnr.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a shekarar 2017 aka naɗa Olateru a matsayin kwamishinan hukumar binciken haɗurra ta wancan lokacin (AIB).

Daga bisa ni aka sauya hukumar ta rikiɗa ta koma NISB kuma aka ƙara faɗaɗa aikin hukumar ya zama alhakinta binciken haɗurran jirgin sama, jirgin ƙasa, hatsarin ruwa da na ƙasa.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige shi daga muƙamin, kuma nan take ya nada Badeh a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Yadda na sha wahala a koƙarin yin gaskiya - Olateru

Da yake jawabi a wurin miƙa ragamar hukumar, Olateru ya ce zai bar NSIB, fiye da yadda ya zo ya same ta lokacin da aka kaɗa shi, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya aike da muhimmin gargadi ga Gwamna Fubara

A kalamansa ya ce:

"Wannan tafiya ce da muka fara tun ranar 17 ga Janairu, 2017, mun ɗauki tsawon lokaci amma abu daya da zan iya cewa shi ne Allah Madaukakin Sarki, mahaliccin sama da kasa, shi ke bada nasara."
"Mun ci baƙar wahala, ni a karan kaina na sha wahala sosai saboda wannan aikin ba shi da sauƙi don haka ba na yi masa hassada. Ga waɗanda ba su sani ba na rasa aurena a wannan aiki."
"An yi mun barazanar kisa sau da yawa domin ina ƙoƙarin yin abin da ya dace. Don haka yana da matukar muhimmanci mu ƙara gode wa Allah a wannan tafiya."

Ya nemi afuwar ma’aikatan hukumar waɗanda watakila ya yi musu laifi a yayin gudanar da aikinsa, yana mai cewa wani lokacin yana iya faɗawa tarkon son rai.

Hukumar JAMB Ta Yi Karin Kudin Jarrabawar UTME

A A wani rahoton na daban Wani sabon rahoto ya yi nuni da cewa hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta kara kudin UTME.

Sabon kudin da dalibai za su biya don zana UTME zai fara ne daga shekarar 2024, inda karin ya shafi jarrabawar mai hade da gwaji (mock) da maras gwaji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262