Innalillahi: Rayukan Mutum 2 Sun Salwanta Bayan Wasu Motoci Sun Yi Taho Mu Gama

Innalillahi: Rayukan Mutum 2 Sun Salwanta Bayan Wasu Motoci Sun Yi Taho Mu Gama

  • An samu asarar rayukan mutum biyu a jihar Ogun a wani mummunan hatsarin mota da ya auku cikin dare
  • Kwamandan hukumar FRSC wanda ya tabbatar da aukuwar hatsarin, ya ce lamarin ya auku ne wajen ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadi
  • Ya tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da wasu mutum takwas suka samu raunuka a yayin hatsarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun ta bayyana cewa mutum biyu sun mutu yayin da wasu takwas suka samu raunuka a wani hatsarin mota.

A cewar hukumar hatsarin ya ritsa da wasu motoci biyu a hanyar Idiroko zuwa Ota a daren Lahadi, 17 ga watan Disamban 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An bankado wata kullalliya da gwamnatin Tinubu take yi wa Peter Obi

An samu hatsarin mota a Ogun
Hatsarin mota ya salwantar da ran mutum biyu a Ogun Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Twitter

Yadda hatsarin ya auku

Mista Anthony Uga, Kwamandan FRSC na jihar Ogun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a Ota, ya ce hatsarin ya auku ne da ƙarfe 8:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uga ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da wata babbar mota ƙirar MAN mai lamba LSR 10 YD da wata mota ƙirar Toyota Carina wacce ba ta da lamba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Ya ce mutum 10 da suka haɗa manyan maza biyar, manyan mata huɗu da kuma ƙaramar yarinya ne hatsarin ya ritsa da su.

Kwamandan ya ce motocin guda biyu sun yi karo da juna ne a bisa kuskure, wanda ya yi sanadin mutuwar manyan maza biyu yayin da wasu mutum takwas suka samu raunuka daban-daban.

"An kai waɗanda suka tsira zuwa babban asibitin Idiroko domin yi musu magani yayin da iyalan waɗanda suka mutu suka tafi da gawarwakin." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya tsige shi, tsohon shugaban NSIB ya tona gaskiyar abinda ya faru yayin aikinsa

An ba masu motoci shawara

Uga ya ce jami’an FRSC sun janye motocin daga kan titi domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a yankin.

Shugaban na FRSC ya gargadi masu ababen hawa da su guji wuce gona da iri kuma ya bukace su da su rage saurin gudu domin su rage aukuwar bala’i a lokacin bukukuwa.

Mutum 12 Sun Mutu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Plateau ya yi ajalin mutane 12 da jikkata wasu fiye da 30.

Lamarin dai ya auku ne bayan wata motar tirela maƙare da hatsi da kuma mutane ta kife yayin da ta ke haurawa a kan hanyar Hawan-Kibo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng