An yi wa mai adaidaita kyautar N100k kan dawo da miliyan 9 a Yobe
- Wani mai adaidaita sahu, Ali Bulama, ya mayarwa fasinja da kudin da ya manta naira miliyan 9 a kauyen Jumbam, jihar Yobe
- An bai wa Bulama takardar karramawa da kyautar kudi N100,000 saboda gaskiyarsa da tsoron Allah
- Mai adaidaitan ya ce mai kudin, mazaunin Maiduguri a jihar Borno ya ba shi kyautar kudi N20,000
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Yobe - An yi wa wani mai adaidaita sahu, Ali Bulama daga kauyen Jumbam, karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe, kyautar kudi N100,000 saboda gaskiyarsa da tsoron Allah.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, matashin mai adaidaita sahun dai ya tsinci kudi naira miliyan 9 sannan ya mayarwa mai shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda na tsinci miliyan 9 na fasinja a adaidaita na - Bulama
Aji Jumbam, mai shekaru 35 ya ce mai kudin, mazaunin Maiduguri ya shiga adaidaitansa a Jumbam da misalin karfe 9:30 na daren ranar 17 ga wata Nuwamba.
Ya ce:
“Da misalin karfe 11:30 ne ko bayan na ajiye shi na koma gida sannan ne na ga wani buhu kunshe da wasu kayayyaki da aka bari a adaidaita sahuna.
“Lokacin da na lura cewa buhun na kunshe da wasu kudade ne, sai na gaggauta fita don neman mai shi. A lokacin, labarin batan naira miliyan 9 din ya rigada ya karade kauyen.
“Bayan dan wani lokaci da taimakon wasu yan kauyen, aka gano mai kudin sannan na mika masa kudin.”
Bulama, wanda ya yo hayar adaidaita sahun, ya ce mai kudin ya ba shi N20,000 a matsayin tukwici.
An karrama Bulama tare da ba shi kyautar kudi
Shugaban kungiyar sakatarorin dindindin masu ritaya na jihar Yobe, Alhaji Maisandari Lawan, ya gabatarwa Bulama da lambar yabo ta karramawa da kudi N100,000.
Alhaji Lawan ya yaba ma dan adaidaita sahun bisa gaskiyarsa da kuma tsoron Allah.
Matashi ya kawata adaidaitarsa kamar mota
A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun yi martani masu ban dariya bayan bayyanan bidiyon wani keken adaidaita sahu da aka kawata shi domin ya yi daban da saura.
Mai adaidaita sahun, @ortiz.1992, ya wallafa wasu jerin bidiyoyi a TikTok don nunawa mabiyansa abun hawan nasa.
An yi wa keken fenti da kaloli masu kyau, sannan aka manna hotunan sitika iri-iri don jan hankalin masu wucewa ko fasinjoji.
Asali: Legit.ng