Matashi Ya Kawata Adaidaita Sahunsa Ta Koma Tamkar Marsandi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
- Wani dan adaidaita sahu ya dauki sana'arsa zuwa mataki na gaba inda ya kawata adaidaitansa ya yi kyau matuka
- Mutumin ya wallafa wasu jerin bidiyoyi a TikTok don nunawa mutane irin kyawu da banbancin adaidaitansa da na sauran mutane
- Masu amfani da soshiyal midiya da dama da abun ya burge su, sun bayyana adaidaita sahun a matsayin karamin Marsandi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jama'a sun yi martani masu ban dariya bayan bayyanan bidiyon wani keken adaidaita sahu da aka kawata shi domin ya yi daban da saura.
Mai adaidaita sahun, @ortiz.1992, ya wallafa wasu jerin bidiyoyi a TikTok don nunawa mabiyansa abun hawan nasa.
An yi wa keken fenti da kaloli masu kyau, sannan aka manna hotunan sitika iri-iri don jan hankalin masu wucewa ko fasinjoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, an sanya wutaye kala-kala da dama a jikin adaidaita, kuma suna ta walwali a bidiyon.
Har ila yau akwai wasu sabbin kujeru a adaidaitan, kuma musamman aka kera su da kaloli masu kayatarwa.
A takaicen takaitawa, mutumin na da katon abun gashe gobara a cikin adaidaitan. an manna shi da kusa kasancewar mutumin na son ganin komai nasa tsaf, kuma mutane sun kira adaidaitan da karamin Marsandi.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Callmepyddo ya ce:
"Adaidaita sunansa adaidaita babu abun da za ku fada mani."
@Shakara ya yi martani:
“A karshe Pablo ya zo gida don bikin Kirsimeti.”
@Chimaobi nelson ya ce:
"Baaba kuma kana tka shi a kasa ko dai a kai kake daukar sa?"
@Rev Sam Jnr ya ce:
"Karamin Benz kenan."
@Israel ya ce:
"Muna kiran shi da adaidaita sahun manyan mutane."
Matashi ya kera motar G-Wagon
A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya wanda ya kera motar G-Wagon ya kai abar hawar tasa gaban wata mai wasan barkwanci (Mama Uka) don ta duba.
Mama Uka ta ce mutane da dama na ta kokarin kushe fasahar mutumin, cewa ya yi amfani da injin din adaidaita sahu ne a motar.
Asali: Legit.ng