Jerin Sunayen Manyan Jami'o'i 20 Mafi Kyau a Duniya Na Shekara Mai Zuwa 2024
- QS World University Rankings ya wallafa jerin fitattun jami'o'i na sahun gaba a muhallin karatu na shekarar 2024 mai zuwa
- Makarantar fasaha ta Massachusetts, jami'ar Cambridge da jami'ar Oxford ne suka mamaye matsayi ukun farko
- Jerin ya ƙunshi makarantu 1,500 daga sassa daban-daban 104 na duniya kuma ya maida hankali ne kan aiki da ɗorewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
London, UK - Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT) ta zama ta ɗaya a jerin manyan makarantun neman ilimi na duniya da aka fitar na shekarar 2024 mai zuwa.

Asali: Getty Images
Hakan na ƙunshe ne kunshin jerin manyan jami'o'in duniya wanda 'QS World University Rankings' ya fitar karo na 20 wanda ya kunshi makarantu 1,500 daga wurare 104.

Kara karanta wannan
Jerin mutane 8 da suka bada taimakon miliyan 700 da aka kashe masu Maulidi a Tudun Biri a Kaduna
Jami'o'in ƙasar Burtaniya guda biyu, Cambridge da Oxford, sune suka zo na biyu da na uku bi-da-bi, wanda ya sa suka zama jami'o'i uku mafi kyau a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
QS World University Rankings, sune kaɗai suka saba fidda jerin manyan makarantu mafi kyau da babu nau'insa a duniya ta hanyar duba ɗaukar aiki da ɗorewa.
Jerin manyan jami'o'i 20 mafi kyau a duniya
1. Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT)
2. Jami'ar Cambridge
3. Jami'ar Oxford
4. Jami'ar Havard
5. Jami'ar Stanford
6. Kwalejin Imperial da ke birnin Landan
7. ETH Zurich
8. Jami'ar Singapore ta ƙasa
9. University College ta Landan
10. Jami'ar California
11. Jami'ar Chicago
12. Jami'ar Pennsylvania
13. Jami'ar Cornell
14. Jami'ar Melbourne
15. Makarantar fasaha ta California
16. Jami'ar Yale
17. Jami'ar Peking
18. Jami'ar Princeton
19. Jami'ar kudancin Wales

Kara karanta wannan
Rikici ya ƙara tsanani, 'yar majalisa ta yi amai ta lashe, ta sauya sheƙa daga APC zuwa PDP
20. Jami'ar Sydney
ECOWAS ta amince zata cire wa Nijar takunkumi bisa sharaɗi
A wani rahoton na daban Shugaban majalisar kungiyar ECOWAS , Sidie Tunis ya ce za a janye takunkumin da aka kakabawa Nijar amma da sharadi.
Sidie Tunis ya yi wannan bayani ne a lokacin da tawagar ‘Africans Without Borders’ ta kai masa ziyara a jiya.
Asali: Legit.ng