MURIC Ta Yabi Tsohon Shugaba Buhari, Ta Bayyana Yadda Ya Ceto Najeriya

MURIC Ta Yabi Tsohon Shugaba Buhari, Ta Bayyana Yadda Ya Ceto Najeriya

  • Ƙungiyar MURIC ta fito ta yabi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan nasarorin da ya samu
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa masu cewa Buhari ya gaza suna yi domin siyasa ko sun manta da tarihi
  • A cewar ƙungiyar Buhari ne ya ceto ƙananan hukumomi 17 na ƙasar nan da suka faɗa hannun ikon Boko Haram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar kare haƙƙin musulmi ta MURIC, ta yabi salon mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ƙungiyar ta ce babu wanda ya isa ya shashantar da kyawawan ayyukan da Buhari ya yi, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya ciri tuta a a cikin tsofaffin shugabannin da suka shuɗe a Najeriya, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka sojoji 4 a wani sabon hari, bayanai sun fito

MURIC ta yabi Muhammadu Buhari
MURIC ta ce Buhari ya yi kokari a mulkinsa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Farfesa Ishaq Akintola, babban daraktan MURIC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC ta yabi Buhari

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mu a ƙungiya ce a kodayaushe muna ganin cewa abun dariya ne duk lokacin da wani ya yi ƙoƙarin shashantar da nasarorin tsohon Shugaba Buhari. Ya ciri tuta a cikin dukkanin tsofaffin shugabannin da suka shuɗe na ƙasar nan."
"Baya ga firaministan Najeriya na farko, Alhaji Tafawa Balewa, tsohon Sardaunan Sokoto, Alhaji Ahmadu Bello da tsohon shugaban mulkin soja, Murtala Muhammed, babu wani shugaban Najeriya da ya kai kishin ƙasa, gaskiya, riƙon amana kamar Muhammadu Buhari."
"Waɗanda su ke ganin Buhari a matsayin ya gaza, ko dai suna yi ne domin siyasa ko suna fama da matsalar cutar mantau. Idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki a lokacin, Buhari ya samu nasarori da dama ga Najeriya."

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta aike da muhimmin gargadi ga Shugaba Tinubu kan karin albashin N35,000

Yadda Buhari ya ceto ƙasar nan a hannun Boko Haram

Jaridar Leadership ta ce Akintola ya bayyana cewa a lokacin mulkin Buhari ne ya ceto ƙananan hukomomi 17 daga cikin 774 da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram.

A kalamansa:

"Amma Buhari ya kore su tare da ƙwato dukkanin yankunan. Sojojin Najeriya da suke guduwa zuwa Nijar ko Chadi a lokacin da ake gwabza ƙazamin faɗa da ƴan tada ƙayar baya saboda rashin ingantattun makamai sun samu karfin gwiwa a ƙarƙashin ɗan asalin Daura."

MURIC ta ce an samu wannan nasarar ne saboda Buhari bai azurta kansa da kuɗaden ƙasa ba, inda a maimakon hakan ya inganta kayan aikin jami'an tsaro.

"Wannan ne ya sa MURIC ta taɓa bayyana Buhari a matsayin uban Najeriya ta zamani. Har yanzu muna nan a kan bakan mu." A cewarsa.

Sanatan APC Ya Faɗi Kuskuren Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya yi magana kan kuskuren da tsohon Shugaba Buhari ya yi a lokacin mulkinsa.

Dan majalisar ya ce an samu barayi da yawa a lokacin da Muhammadu Buhari ya ke karagar mulki tsakanin shekarar 2015 da 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng