Dabara Ta Kare: 'Yan Sanda Sun Kama Shaharrun Masu Satar Mota a Jigawa

Dabara Ta Kare: 'Yan Sanda Sun Kama Shaharrun Masu Satar Mota a Jigawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wasu shahararrun barayin mota da suka addabi jihar da makwaftan ta
  • Rundunar ta samu korafin satar motar wani likita a jihar, wanda ya kai su ga kama barayin tare da kwato wasu motoci uku
  • Haka zalika, rundunar ta ce wadanda aka kaman sun amsa laifin su, inda za a gurfanar da su gaban kotu da zaran ta gama bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Jigawa - A ranar Talata, 12 ga watan Disamba, rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta sanar da cafke wasu shahararrun masu satar mota a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Abubakar Isah ya sanar da hakan a garin Dutse, inda ya ce an kwace motoci uku a hannun barayin bayan kama su.

Kara karanta wannan

Cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa a karo na uku

Rundunar 'yan sanda ta kama barayin mota a Jigawa
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta ce wadanda aka kaman sun amsa laifinsu tare da tabbatar da cewa sun dade suna satar motoci. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

ASP Isah ya bayyana cewa a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2023 da misalin karfe 8 na dare, wani Dr Abdullahi Dogo ya shigar da karar sace motarsa a kasuwar Yantifa da ke Dutse.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Dr Abdullahi Dogo ya ce an sace motarsa mai lamba KHS 96 AA JIGAWA, kalar toka a kasuwar Yantifa da ke karamar hukumar Dutse.

Isah ya ce a ranar 21 ga watan Nuwamba, misalin karfe 10 na dare, suka fara bin diddigin mota kirar FAW VITA, kalar toka mai lamba KWL 274 AS ABUJA, rahoton Daily Trust.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wasu mutum biyu, Abdullahi Sani da Faruk Adamu, inda aka samu makullai tara, lambobin mota daban-daban da wasu kayayyakin da suke bude motoci.

Ya kara da cewa wadanda aka kaman sun amsa laifinsu tare da tabbatar da cewa sun dade suna satar motoci, inda aka gano motar Dr Abdullahi Dogo a wajensu.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun yi ajalin kasurgumin dan ta'adda, Kachalla, sun hallaka kwamandojin Dogo Gide 3

"Dukkanin wadanda aka kama suna tsare hannun sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ke Dutse, inda za a gurfanar da su gaban kotu da zaran an gama."

A cewar Isah, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Yan sanda sun kama masu laifi 130 a jihar Katsina

Daga jihar Katsina kuwa, Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 130 a cikin wata daya a jihar.

Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi da makami 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69, kamar yadda rahoton Leadership ya nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Tags: